DSS ta sako kafinta bayan gano ba shi da hannu a sace ‘yan makarantar Oyo, ta biya diyyar miliyan N3

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta saki wani kafinta mai suna Mustapha Marwana, wanda aka kama bisa zargin sa da hannu a garkuwa da halaka ɗalibai da malaman wasu makarantu a yankin Oriire da ke Jihar Oyo.

Darakta Janar na hukumar, Tosin Ajayi ne ya bayar da umarnin sakin nasa bayan masu bincike sun wanke shi daga dukkan wani abin da yake alaƙanta shi da harin.

Wata majiyar tsaro da ke da kusanci da batun ta ce kwamitin binciken DSS ya gudanar da bincike mai zurfi akan zargin Marwana da hannu al’amarin kana daga bisani da wanke shi.

Kwamitin ya gano cewa, Marwana, wanda Bakatsine ne, bai kasance mamban kowacce ƙungiyar ta’addanci ba kuma ba shi da wata alaƙa da ƙungiyar Ansaru da aka ɗora wa alhakin farmakin.

Akan haka ne daraktan hukumar ya umarci a gaggauta sake shi da kuma ba shi Naira miliyan 3 a matsayin diyya domin tallafa wa sake gina rayuwarsa. Majiyar ta ƙara da cewa, Marwana ya bayyana godiyarsa ga Tosin Ajayi yana mai bayyana shi a matsayin jajirtacce kuma mai tausayi.

Wannan wani ɓangare ne na matakan da jagorancin DSS na yanzu ke amfani da shi wajen lallashin waɗanda aka wanke su daga tuhumar aikata laifi don ƙarfafa musu wajen dawo da karsashinsu acikin al’umma.

A ranar 15 ga watan Mayu ne wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru ne suka kai farmaki a makarantun Community Grammar School, Baptist Nursery/Primary School da L.A. Primary School da ke Oriire, inda suka yi awon-gaba da ɗalibai 39 da malamai bakwai.

An halaka biyu daga cikinsu kana daga bisani sauran mutanen suka shaƙi iskar ‘yanci a ranar 10 ga Yuli bayan wani atisaye da sojoji suka ƙaddamar.

By Babaji

Leave a Reply