Dubban likitoci ne suka garzaya Shanghai don taimaka wa birnin wajen yaƙi da COVID-19

Daga CMG HAUSA

Rahotanni daga ƙasar Sin na cewa, kimanin likitoci 10,000 a duk faɗin ƙasar ne, suka garzaya zuwa Shanghai, cibiyar kasuwanci ta ƙasar, domin taimakawa cibiyar wajen daƙile yaɗuwar annobar COVID-19.

Jiya Lahadi, dubun dubatan likitoci ne, suka isa birnin Shanghai mai yawan jama’a miliyan 25 ta cikin jiragen ƙasa masu saurin tafiya, wadanda suka taso daga yankunan Tianjin da Hubei da Shandong da Jiangxi.

Hukumar lafiya ta birnin Shanghai ta bayyana cewa, tun da farko akwai tawagogin likitocin da suka fito daga lardunan Zhejiang da Jiangsu da Anhui da ke kusa, da suka riga suka isa birnin domin shiga aikin yaƙi da annobar.

A ranar Asabar din da ta gabata, mahukuntan birnin Shanghai sun ba da rahoton mutane 438 da aka tabbatar sun kamu da cutar ta COVID-19 a cikin gida, da kuma mutane 7,788 da suka kamu da cutar ba tare da nuna alamu ba.

Mai fassara: Ibrahim Yaya