Matan da ba su samu mijin aure ba (1)

Daga AISHA ASAS

Daga lokacin da mace ta balaga, za ka ji ana mata addu’ar samun mijin aure. Yawaitar wannan furuci tsakanin dangi kan yi tasiri ga wasu yaran wajen tsaya wa da samarin da ke neman aurensu. A ganinsu ba abinda ya fi dace wa da su da ya wuce samun mijin aure.

Ba wai na ce hakan laifi ba ne, sai dai a inda gizo ke saqa shine, lokacin da yarinyar ta kasa samun mijin aure. Matsin lambar da yarinya ke samu a lokacin da ta kawo ƙarfi daga baki da fuskokin mutane na ɗaya daga cikin dalilan da ke sata a ƙunci ba rashin auren kawai ba.

Idan ya kasance duk lokacin da macen da ta isa aure ba ta samu miji ta shiga mutane zancen aure ake mata, sai ta ga ta fita daban, zuciyarta ta raya mata ana ganin laifinta ne, wani lokacin ma ba raya mata ta ke yi ba, mutane ne ke binta da kalaman. To fa a wannan lokacin sai ta fara shirin amsar aure ido rufe.

Sau da yawa za kaga macen da ta fara shekaru a gida, idan wani ya zo nemanta, lokacin da aka gano yana da wata matsala, sai ka ji tana ƙoƙarin amincewa da ita. ita dai ayi auren ko na kwana biyu ne ta fito, hakan zai sa ta fita layin ‘daushen goro’ kamar yadda ake kiransu, ta koma bazawara. Shin me ke sa mata a wannan turbar? In ce bakin mutane.

A nan ina so in yi tambaya ga su masu ganin laifin matan da ba su yi aure ba. Shin mace ke hurumin neman aure ko namijin ne ke fara tayawa? Idan kuwa kun amince namiji ne, to ina laifin macen da ba ta samu wanda ya zo nemanta da zumar aure ba.

Wani abin haushi da takaici, idan yarinya ta ƙi kula samari, sai a ce ba ta son aure. Idan ta kula su, ba ta yi auren ba, sai a ce ta ƙi aure. Anan mutane sukan manta abu biyu. Na farko, rashin kula samari ba shi ne dalilin da zai hana mace aure ba, domin idan lokacin auren ya zo, sai ta amince da wanda aka ƙaddarta ya zama mijinta. A lokacin da ta ke kula samari kuwa, mu kan manta cewa, ita ko ta tsaya da niyar tsayar da mijin aure, shi saurayin da ya zo kun san ta sa manufar?

Idan aka ga mace ta tsaya da saurayi, kwana biyu ta kore shi, sai a ce dama ba auren ta ke so ba yaudara ce, ko shashanci ta sa a gaba. Shin kun tava zurfafa tunaninku don tabbatarwa kafin ku zargeta. Kun taɓa tambayar kanku shi da ya zo, da me ya zo. Sau da yawa samari na shiga cikin rigar aure, su zo neman mace, amma fatansu ta sake da su, su isar da mummunar manufarsu kan ta. To idan an yi sa’a da mutuniyar kirki, da ta gano nufinka, sai ta ce Umma ta gaida Aysha. To ina wannan ta cancanci zagi ko zargi.

Irin kallo da maganganun da kuke mata ne ya sa ta ke neman miji ruwa a jallo, shi ya sa ta ke kula duk wanda ya furta kalmar so gare ta, don fatan a yi dace ta amerce. Sai dai lokacinta bai zo ba, shi yasa mijin ya maƙale wani wurin. Anan me ake so ta yi. Ta kai kanta ɗakin miji ko ta tursasa wani dole sai ya aure ta.

Abu na biyu da mutane suka kasa fahimta ko suka kawar da kai kan sa don son zuciya shine, shi aure tamkar rayuwar ɗan Adam ce. Lokacin yin sa da kuma lokacin rabuwa duk rubutace ne. sai dai wasu ababe da ke bi ta tsakani don su zama sila. Yadda ba za ki iya sanin ranar mutuwarki ba, haka ba za ki iya sanin rana da kuma wanda za ki aura ba har sai lokacin ya yi.

Na san za ku amince da furucina, domin ba ɓoyayen lamari ba ne, an saba ganin auren da aka kitsa yinsa shekaru masu yawa, amma sai lokaci ya yi a yi da wani. Kuma an saba girka soyayya mai zafi tsakanin saurayi da budurwa tsayin shekaru, har iyaye su yi masu alƙawarin aure, kai wani karon har tabbatar da zancen ake yi ta hanyar gabatar da wasu daga cikin al’adu ko sharuɗan aure, amma daga ƙarshe sai a fahimci matar wani ce ya ke yi wa hidima, ko mijin wata ce take labta wa kalaman soyayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *