Sharhin littafin ‘Duhun Damina’ na Maryamerh Abdul

Daga BAMAI ALHAJI DABUWA

Sunan Marubuciya: Maryamerh Abdul
Shekarar Bugu: Babu.
ISBN: 978-978-982-968-4.
Mai Sharhi: Bamai Dabuwa.
Lambar Waya: 07037852514.

Gabatarwa/Abubuwan Burgewa:
Littafin ‘Duhun Damina’ littafi ne da a ka yi amfani da wani irin salo mai kama da tafiyar kura. Shi ne littafin da ya kawo zunzurutun kuɗi sama da miliyan guda a ranar da a ka ƙaddamar da shi. Littafin ya taɓo wata matsala da kusan kowa ke tsoron taɓawa saboda gudun tambayar kai ta ya aka yi ka sani? Wasu kuma hankalinsu bai kai wajen ba, musamman iyaye, amma kuma rayuwar ‘ya’yansu ce dumu-dumu a ciki. Littafi ne da kowanne uba/uwa ya kamata su karanta domin fahimtar rayuwar yara. A taƙaice littafin ya yi magana ne a kan Istimna’i ((Sexual self satisfaction ko Musturbation). Littafin ya yi magana a kan abubuwan da yake haifarwa duk da cewar binciken likitoci ya gwada ba shi da wata illa ga jiki. Ya yi bayani kan hange da matsayar Malamai, inda wasu suke ganin haramun ne wasu kuma suka halatta. Ban taɓa sanin cewa akwai yanayin da giya da mushe suka halatta wa Musulmi ba sai da na karanta wannan littafi. Yana da kyau iyaye, samari da ‘yan mata su karanta wannan littafin.

Tsokaci: 
Shi rubutu musamman na zube yana da wasu ƙa’idoji da tsare-tsaren da ake bi wajen gabatar da shi. Gaskiya ne cewa ana yinsa ne wani loton don faɗakarwa, a wani wajen kuma Ilmintarwa, nishaɗantarwa da saura ko kuma gamayyar duk a kuma littafi guda. Sai dai mu sani ya sha bamban da wa’azi ko koyarwa ko Insha’i. Ke nan dole domin yinsa da kyau akwai buƙatar kiyayewa da binsa yadda yake a tsari. Kuskure ne kai tsaye a isa wajen da ake son zuwa tun daga farko. Akwai buƙatar saƙa matsala, tsawwalata da kuma warwarewa. Tun ba a je ko’ina ba a wannan littafi mai shafi 200, daga shafin farko zuwa na talatin an bai wa mai karatu matsala, abin da take haifarwa da kuma warwara (wato bari). A wa’azance an samu abin da ake so. Amma a tsari na zube an so a tsawwala matsala kuma a riƙe mai karatu da ruɗu kar a ba shi abin da ake so ko yake so har sai ya je ƙarshe. A taƙaice mutum ba ya buqatar ci-gaba daga shafi na 30, domin duk wani saƙo da ake buƙata ya isa a wannan tsakanin. ‘The book is much more of an essay than a story’. Kana daga cikin kuskure ko raunin da wannan littafi ya samu yadda ake gabatar da al’amuran taurarin da kuma tafiyar labari kara zube. Haka kawai sai ka ɗauka a jami’a ake sai ka ga ba haka ba sama ta ka. Salon labari tafiyar kura salo ne dake zuwa ya dawo. Daga cikin abubuwan da ake so masa domin ya cika, dole ya kasance gaban ba zai tafi ba ne sai an danganta da bayan. Ko kuma bayan na ɗauke da wani muhimmin abu da zai warware gaban. Sannan akwai buƙatar samar da ganɗoki a gaba da bayan. Ta yadda mai karatun zai so a koma bayan kamar yadda zai so kuma a cigaba. 

Kura-kurai:

  1. Kuskurewa Daidaitacciyar Hausa.
    An samu kuskure sosai na Hausar baka a labarin kuma ba a ƙaulin taurari ba da kuma cewar salon da aka zaɓa wajen bayar da labarin salo ne a wajen fage. Misali:
    A. Yanda maimakon yadda (shafi na 3).
    B. In maimakon idan (shafi na 3).
    C. Ratsa sa maimakon ratsa shi (3).
    D. Kashe sa maimakon kashe shi (3).
    Da saura…
  2. Kuskuren ƙa’idojin Rubutu.
    Ya zo a littafin, wurare da dama da marubuciyar ta kuskurewa yadda ya kamata a rubuta wasu kalmomin daidai. Daga ciki akwai misali kamar haka:
    A. Waresu maimakon ware su (shafi na 3).
    B. Ratsasa maimakon ratsa sa ko ratsa shi (shafi na 3).
    C. Kafeta maimakon kafe ta (4).
    D. Akan maimakon a kan (5).
    Da saura…
  3. Kufcewar Salo:
    Kasancewar labari ne da aka rubuta cikin harshen Hausa, kuma domin makaranta Hausawa, ke nan kuskure ga marubuciyar idan ta zaɓi fassara ko sauƙaƙa wata kalmar ko jimlar ta Hausa zuwa wani harshen daban. Misali:
    “,wurin wanke hannu (wash hand basin) da ke banɗakin.” (4, har’ilayau duba shafi na 5, 9 da saura…).
    Sannan kuskure ne saka alamar zancen wani (ƙauli) da motsin rai a maganar da ya zo a wajen fage kamar yadda marubuciyar ta yi a shafi na 16 kamar haka:
    “He is addicted!”

3.1. Jirkiɗa Jinsin Wasu Kalmomin Daga Mace Zuwa Namiji Ko Savani. Misali:
“Mummunar ciwon kai.” (4. Har’ilayau duba shafi na 5, 7 da saura).
3.2. Savani/Tsallakewa Da Rubuta Kalma Daidai. Misali:
“,saman ofishin ɗan daidaita nutsuwarsa.” (4).

3.2. Amfani Da Sanya Alamomi A Inda Ba Wajensu Ba.
“Kai tsaye wurin motarta ta yi ta shige gudun haɗuwa da ƙawayen… ƙawayenta?” (6).
Babu buƙatar alamar zarce da tambaya a wannan jimlar.

3.3. Sakin Salon Da Aka ɗauka Zuwa Wani Salon Cikin Kuskure:
“Shin ya zai yi ya shawo kan wannan matsalar da ya kunna masa wuta da hannuna.” (14).

3.4. Wai matar da a shafi na 6 ta manta komai a ɗakin jarabawa har ma ta saduda ta yi submitting ta fita. Ita ce kuma wai a shafi na 7 take sa ran samun B a jarabawar. 

3.5. Ya zo a wurare dayawa inda mahaifiyar Juwairiyya ke kiran ta da sunanta kai tsaye (14, 31, 32, 33), kwatsam a shafi na 35 muka tsinci mahaifiyar na kiranta kamar haka:
“Hamrah! Tashi ki sha maganinki.” Kuma babu inda a baya aka bayyana hakan a matsayin wani sunan na Juwairiyya.

3.6. Kuskurewa Azanci Ko Abin Da Hankali Zai ɗauka.

Ya zo a shafi na 36 kamar haka:
“Tun rasuwar mijinta, duniya ta juya musu baya, arziƙin da suke tunanin yana dashi duk ya ƙare wurin biyan bashin qudin banki da ya ci, wanda ya yi sanadiyyar sayar da gidansu na Abuja, da sauran ƙananan kadarorinsa da suke tunanin zai iya riƙe su.”
A nan mun fahimci talakawa ne su ashe. Amma kuma a baya, shafi na 6 kamar haka:
“Cikin kwanciyar hankali ta shiga motarta ta fice daga gidan a hankali…”

Ka ji fa! Mutanen da suka siyar da duk wasu kadarori manya da ƙanana.

3.7. Mun fahimta daga shafi na 10 zuwa na 13 Abdul ne saurayin Juwairiyya.
Sai kawai a shafi na 37 ya zo haka:
“Daga lokacin da Salman ya amsa tayinta, ta sa a ranta…”

3.8. Mun fahimta a shafi na 36 cewa mahaifin Juwairiyya ya mutu. A shafi na 53 kuma sai muka tsinci mahaifiyar Juwairiyya ɗin na cewa kamar haka:
“Ya zama dole ta sanar da mahaifinta don a bata dama ta kawo mijin aure.” (Har’ilayau duba shafi na 55).

  1. Kuskuren Bugu Ko Aikin Computer:
    An samu maimaici wasu sakin layi har biyu sau biyu a shafi na 10 da 11.
  2. Kuskure Wajen Gabatar Da Canji Na Rayuwar Taurari Yadda Ya Kamata:
    A farko mun fahimta Juwairiyya ‘yar makaranta ce (6) sai kuma kwatsam a shafi na (38) har ta gama tana aiki ma. Sannan ɓaro-baro ya kuma dawo mana a shafi 43 kamar haka:
    “I love you (ina sonka) Abdulwahab ɗina!”

5.1. Babu inda marubuciyar ta siffanta mana siffar Juwairiyya idan ka ɗauke kasancewarta bakar fata. Amma sai ta riƙa tunatar da mu surarta a wurare dayawa daga ciki akwai shafi na 61.
“Duk da kasancewarta mai halitta irin wannan.”
Wacce halittar?

5.2. Mun fahimta cewa Juwairiyya ta fara istimna’i tun tana da shekaru 15 (59 & 62) ta hanyar zurkuɗa hannunta a farjinta a karon farko har ta samu gamsuwa. Amma ba ta rasa budurcinta ba. 

Marubuciya Maryamerh Abdul

Tambayoyi:

  1. Ya zo a shafi na huɗu kamar haka cikin alamun ƙauli:
    “What’s wrong with you Abdulwahab? (Me ke damunka Abdulwahab)?”
    Shin bayan ya furta da Turancin ne kuma ya fassarawa kansa ko ya abin yake?
  2. Shin kalmar ƙofa ba mace ba ce, me ya sa ya zo haka a shafi na 4?
    “…inda ƙofar yake.”
  3. Tambaya wane kalar yawu ne mai tauri? (18).
  4. A shafi na 26-27 bayan an yi bayani kan matsayar Malamai kan halacci da haramcin istimna’i. Sai marubuciyar ta faɗa kamar haka cikin ƙaulin tauraron a shafi na 27:
    “Saɓanin Malamai alheri ne.”
    Ke nan duk wanda mutum ya zaɓa cikin biyun (halal/haram) daidai ne?

Ƙarewa:

Tsakani da Allah ba sai an faɗawa mai karatu ba, idan ya karanta wannan littafi zai tabbatar da cewa an sha wahala da matukar bincike kafin kammaluwar wannan littafi. Marubuciyar ta yi matuqar ƙoƙarin burtso da komai da fayyace shi. Babu abin da za mu ce sai dai Allah ya saka mata da alheri.

Shahararren Malami kuma fasihi a duniyar adabi Farfesa Ibrahim Malumfashi ya taɓa faɗa cewa, a kowane labari akwai marubucinsa a ciki. Wannan ya sa min tunanin ina Maryama take a wannan labari na ‘Duhun Damina’?