Boko Haram sun kwantar da sojoji 11 a Kaduna

Daga BASHIR ISAH

Sahihan bayanan da suka riski Blueprint Manhaja a ranar Talata sun nuna mayaƙan Boko Haram sun kai mummunan hari Litinin da ta gabata a wani sansanin soja da ke yankin Polewire a Birnin Gwari, jihar Kaduna inda suka halaka sojoji 11 tare jikkata wasu 19.

Haka nan, harin ya laƙume rayukan wasu ‘yan bangan yankin su uku tare da raunata biyu daga cikinsu.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa, an shafe sama da sa’o’i uku ana ba-ta-kashi tsakanin ‘yan bindigar da sojoji, inda a ƙarshe ‘yan ta’addan suka ƙona motocin yaƙi guda uku mallakar sojojin Nijeriya.

Bayanan tsaro sun ce yankin da lamarin ya faru da ma nan ne ya zamana babbar hanyar da ‘yan bindigar ke bi suna ƙetarawa daga Neja zuwa Zamfara.

An ce baya ga rasa rayukan wasu jami’ai, haka nan sojojin sun yi hasarar kayan faɗa da dama da suka haɗa da motoci da bindigogi da alburusai da babura da sauransu.

Sai dai bayanan da suka fito a kan harin ba su nuna adadin rayukan da aka rasa a ɓangaren ‘yan bindigar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *