Da fim ɗin ‘Munkar’ aka fara kafa kasuwanci da buɗe harkar saida fim a kasuwa – Khalid Musa
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Idan ana dara fidda uwa ake. Idan ana maganar Finafinan Hausa a masana’antar fim ta Kannywood dole ne a sanya Malam Khalid Musa, yana ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa masana’antar Kannywood shekaru 40 da ta gabata. A tattaunarsa da wakilanmu a Kano, Ibrahim Hamisu, za su ji cikakken tarihinsa da kuma yadda ya samu kyaututtuka da dama a Kannywood ciki har da fim ɗin ‘Kadaura’ a shekara 2005. ku biyo mu, don karanta yadda hirar ta kasance:
MANHAJA: Za mu so ka gabatar mana da kanka?
MALAM KHALID: Sunana Khalid Musa wannan ne sunan da a ka fi saninsa a waje, amma kuma ina amsa sunan Haladu Musa a zamanin karatuna da wurin aiki.
Ba mu taƙaitaccen tarihinka?
An haife ni a shekarar 1962 kamar yadda takardu na ke nunawa a garin Burum-Burum ƙaramar Hukumar Tudunwada Dankadai. A lokacin a ƙauyuka babu takardar haifuwa don haka kiyaye shekaru na da wahala. Sai dai ina zaton shekaruna sun ɗan haura haka kaɗan, don ina iya tunawa a lokacin ƙidaya ta shekarar 1973 mahaifina ya bayar da amsar shekaruna da cewa an haife ni ne a 1960. Alakullihalin shekaru 63 ko 65 ai babu yawa idan alheri su bai yawaita ba. Ina roƙon Allah S.W.T ya yi albarka cikin shekarun rayuwarmu.
A Burum-Burum na yi firamare 1969-1975 sannan na tafi Kwalejin Rumfa daga 1975 zuwa 1980. Na ɗan taɓa aiki da kamfanin masaka na Gaskiya da ke Bompai Kano na watanni uku kaɗai, wato Nuwamba 1980 zuwa watan Maris 1981. A ranar 16 ga watan Maris 1981 na fara aiki da Gwamnatin Jihar Kano wanda na kammala shi a 2016 shekara kusan tara kenan.
Na fara aiki ne kai tsaye da bari na makarantar sakandare wannan ya sa ban yi dogon karatu ba, akasarin karatukan da na yi na horon aiki ne. Misali na karatun akwai wanda na yi a makarantar School of Management a studies a 19i1, sannan na sake komawa wannan makarantar dai a 1986-87 na yi karatun Eɗecutiɓe Officer’s Course. A 1989 a ka sake tura ni karatun Public Administration a Jami’ar Bayero (lokacin diploma suke a fannin ba su fara digiri ba) wanda na kammala a shekarar 1992. Ina cikin zaman jarrabawar ƙarshe a lokacin Allah yayi wa mahaifina rasuwa. A yanzu haka ni magidanci ne da ‘ya’ya tara biyar mata, huɗu maza.
A wacce shekara ka tsunduma harkar finafinan Hausa?
Na fara jarraba rubutu tun ina ɗan sakandire aji biyu inda na ajiye wani littafi da na ke rubuce duk wani muhimmin abu da ya faru game da ni lokacin da na je gida hutu. Amma da sunan samar da littafi wannan na fara ne a shekar 1981 inda na rubuta wani wasan kwaikwayo mai suna ‘Rubutaccen Al’amari’. Sai dai ba a buga shi ba, na kai shi kamfani Gaskiya Corporation Zariya a shekarar 1982. Ina zaton har yanzu kwafin na can.
Kana cikin jigo a masana’antar Kannywood. Ta yaya ta samo asali?
Ba jigo kaɗai ba, ina zaton mu muka haifar da ita a matsayin masana’anta. ƙungiyoyin wasannin kwaikwayo ne tushen Kannywood domin waɗanda suka fara jarraba ɗaukar faifan bidiyo na wasanni su ne waɗannan ƙungiyoyi. Amma farko a sahun gaba ƙungiyar Gyaranya ce. Ba na jin akwai waɗanda suka rigaye su wajen fara amfani da fasahar ɓideo su ɗauki wasanninsu. Sun yi finafinai da dama amma babu ɗaya da ya bayyana saboda a lokacin ba wanda yake tunanin za a iya samun kuɗi da harkar. Idan sun yi sai dai su sa a gaba su kalli kayan su su kaɗai. Dalilin saɓanin ra’ayi ƙungiyar Gyaranya ta rabu gida biyu. Daga cikinta aka sami wasu cikin ‘ya’yanta suka haɗe da wata ƙungiya ta Hausawa (O.M.C.) zoo road suka samar da ƙungiyar Jigon Hausa. Hakanan daga gyaranya dai a ka sami ƙungiyar Jan Zaki.
Duka waɗannan ƙungiyoyin sun ci gaba da yin fim tun kafin fim ya zama sana’a. Misali mu a Jigon Hausa mun yi finafinai guda uku daga 1985-86. Finafinan su ne ‘Sanda Jan Namiji’, ‘Ganin Hadarin Nesa’, da kuma ‘A San Na Kamawa’. Sannan akwai ƙungiyar Tumbin Giwa wacce ita ce ƙungiya ta farko da ta fara mayar da fim sana’a. Sannan akwai ƙungiyar Dabo, su ma sun fara fim tun a waccan sahun na kafin ya zama sana’a. Kungiyar Tumbin Giwa ce su ka fara daukar fim su kai kasuwa, amma Jigon Hausa su ne suka fara buɗe kasuwar fim ɗin Hausa ta bunƙasa. Su suka fara buga fim a yi masa kwali na musamman a fim ɗin su mai suna ‘Munkar’. ‘Munkar’ ne fim na farko da ya tayar da kasuwancin finafinan Hausa. Da shi ne a ka fara kafa kasuwancin da buɗe harkar sai da fim a kasuwa. A cikin sati biyu a ka sayar da kasset dubu ɗaya abinda ba a taɓa samu ba gabanni. Don haka waɗannan ƙungiyoyi musamman Gyaranya, Tumbingiwa, Jigon Hausa, Dabo su ne turaku da kuma ginshiƙin samar da masana’antar Kannywood.
Ka ƙware a fagen rubuta labarin fim. Ya za ka kwanta finafinan shekarun baya da da na yanzu a Kannywood?
Ta fuskar labari har yanzu finafinan da a ke yi ba su kai ƙarfin labarin na baya ba, amma aiki da kayan aiki babu gwaji. An cigaba sosai wajen ɗaukar hoto da kayan aiki ba kamar zamanin da ba.
Ka gamsu da irin da yadda ake rubutun fim a wannan lokacin da fim mai dogon zango ya zama yayi?
Shi rubutu fasaha ce, ita kuma fasaha gudana take don haka ba ta taƙaita a wani zamani kaɗai ba. Har yanzu za ka ga finafinan da an yi ƙoƙari ƙwarai wajen rubutu amma irinsu kaɗan ne. Wasu ka na iya zama ka kalle su har ma su ɗauke hankalinka, wasu kuma ko minti goma ba ka iya yi kana kallon su. Wannan gazawa ce da rubutu ke haifar da haka.
Me ya sa finafinan kuduncin ƙasar nan suka fi karɓuwa a duniya, mu ba mu da labarai ne koko?
Fifikon ba a labari ba ne, a ƙarfin jari ne. Idan ta labarai ne finafinan Kudu ba su da labaran da su ka kai namu a ƙarfi. Amma suna zuba kuɗaɗe ma su yawa a fim da kasuwancin sa. Sun yi ƙoƙari sun gina kasuwar finafinan su tun daga cikin gida har zuwa wajen Nijeriya don haka a yau za ka ga sun mamaye kasuwar fim ta Afirka gabaɗaya.
Wai wacce irin rawa ce marubuci ke taka wa a fim?
Rawar da marubuci yake takawa a fim ita ce mafi girma. Kamar dai kirarin nan da ake cewa, ‘rana mai raba wa kowa aiki’, to haka marubuci yake. Idan babu rubutu babu aikin fim gabaɗaya har da kasuwancin sa. Duk girman masana’antar fim tsinin alƙalamin marubuci ne ke ɗauke da ita.
Mene ne bambanci tsakanin rubutun fim da na radiyo?
Abu ɗaya ne kawai ya bambanta su, radiyo kacokan ya dogara ne ga sauti, don haka marubucin radiyo na karkatar da rubutun sa ta hanyar sauti ne kaɗai, amma marubucin fim yana amfani da sauti da gani ne wajen isar da saƙonsa. Amma mafi ƙarfi da tasiri a fim ita ce kafar gani ba ta ji ba, don haka duk abinda za a iya nuna shi a gane ba tare da magana ba, to ba ka buƙatar zance a wurin sai dai a na iya gwama shi da sautin da zai iya fito da da fassara hoton sosai a fahimta. Misalin sautin wuƙa idan ana wasa ta ko na faɗuwar wani abu, ko na kaɗawar iska, waɗannan su ake kira ‘sound effects’.
Waɗanne irin nasarori za ka iya cewa ka samu daga lokacin da kuka fara harkar fim zuwa yanzu?
Ba zan iya cewa ban samu nasara ba, sai da ba ta kuɗi ba. Kasan sunna ce ta rayuwa ka sami wanda ya kafa abu ba shi ne ke cin moriyar abinda ya kafa ba. Kamar dai ɗan dabino ne, ba kasafai mai shukarsa kan amfana da shi sosai ba. Har yanzu ina kallon fim ɗin ‘Munkar’ shi ne mafi girman nasarata domin tasirin da ya yi ga zukatan waɗanda fim ɗin ya shafa. Kar ka manta burin kowane marubuci ne ya ga saƙonninsa sun yi tasiri a zukatan al’umma domin wannan ce manufarsa ta farko a rubutu. Na sami kyautar Gwarzon Marubuci da fim ɗin ‘Kadaura’ a gasar yahoo award ta 2005 sannan da fim ɗin ‘Kadaura’ dai mu ka sami kyautar Gwarzon finafinai na harshen ƙasa a gasar finafinai ta ƙasa da a ka yi a shekarar 2004 cin dai a Abuja, wacce wannan gasar ita ce yanzu a ke kira da Zuma Film festiɓal. A dalilin haka gwamnatin Kano ta larrama mu da takardun yabo a gidan Gwamnatin Kano shekarar 2005. A shekarar 2007 na sami Gwarzon marubuci na shekara a wata gasar finafinai da cibiyar BOBTɓ suka shirya a Abuja. Waɗannan na kadan daga nasarorin da zan iya cewa na samu.
Waɗanne irin ƙalubale ne suke addabar Kannywood?
Babban ƙalubale da ke addabar Kannywood shi ne ƙarancin jari da kuma gazawar hukuma ta samar da wani tsari (policy) da zai tabbatar da bunƙasar masana’antar. Idan babu wani ‘policy’ da zai bai wa mai zuba jari kariyar tabbacin kuɓutar jarinsa zai wuya a samu wasu su tsallako su zuba jari a Kannywood. Idan kuwa jari bai zo ba to ina shakka idan masana’antar za ta iya bunƙasa da kanta ita kaɗai. A halin yanzu Kannywood ta yi girman da ta fi ƙarfin jarin da ke juyawa a cikinta.
Mene ne muƙaminka a ƙasa ko jiha a kannywood?
Ni marubuci ne mai shiryawa amma idan a zubin ƙungiya kake nufi to zan iya cewa na riƙe muƙamai da can baya amma yanzu mun zama iyaye. Ni member ne na Hukumar Amintattu (Board of Trustees) na haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu sana’ar fim ta Nijeriya mai suna MOPPAN (Motion Picture Practitioners Association of Nigeria).
