Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Idan Allah ya hukunta nan da awoyi kaɗan, al’ummar Musulmi da suke sassa daban-daban na duniya, za su ɗauki azumin watan Ramadan, wata na tara a shekarar Musulunci. Kamar yadda malamai suka karantar da mu, watan Ramadan na daga cikin watannin Musulunci masu daraja da ɗimbin alkhairai da ake buƙatar muminai su mayar da hankali wajen ibada da addu’o’i, domin dacewa da rahamar Allah Ubangiji.
Watan Ramadan a cikinsa ne ake gudanar da azumin kwanaki 30 ko 29, inda a cikin waɗannan kwanaki, musulmai maza da mata da suka kai shekarun balaga, kuma suke da cikakkiyar lafiya, za su ƙauracewa cin abinci da shan ruwa, da jima’i, da duk wani aiki da Allah Ya haramta, daga fitowar alfijir zuwa faɗuwar rana. Wannan shi ne azumin da aka wajabta wa al’ummar Musulmi mabiya addinin Annabi Muhammadu (SAWA), a ko’ina suke a duniya.
Daga cikin abubuwan da Musulmi suke shagaltuwa da su a lokacin azumi, sun haɗa da tilawar karatun Alkur’ani Mai Girma, yawan nafiloli da zikirori, don neman ƙarin kusanci da Allah. Sannan a cikin watan ana yin sallolin dare na Tahajjud da kuma Ittikafi, a ranakun goman ƙarshe. Akwai kuma tafsirai da ake gudanarwa a masallatai daban-daban, inda malamai da limamai ke gudanar da sharhi da fassarar ayoyin Alkur’ani Mai Girma.
Abubuwa biyu ne suka fi zama ƙalubale a irin wannan lokaci, wanda malamai da shugabannin al’ummar Musulmi ke ta ƙoƙarin ganin an samu fahimta a kansu, sun zama tarihi. Waɗannan abubuwa kuwa su ne batun ganin wata da sukar juna a tsakanin malamai yayin gudanar da tafsirai. Kodayake ana samun cigaba da sauye-sauye da dama, kuma jama’a na amsa kira, ana samun raguwar bambance-bambance wajen ɗaukar azumi. Amma inda har yanzu ake samun rabuwar kai shi ne wajen aibata juna da sukar aƙidu ko fahimtar wasu mutane a game da addini ko rayuwa. Hakan kuwa a cewar manazarta yana haifar da rabuwar kai, da rashin jituwa a tsakanin mabiya.
A cikin wannan mako mai ƙarewa, na halarci buɗe tafsirin Babban Limamin Jos, Sheikh Ghazali Ismail Adam, wanda yake gudanarwa a Babban Masallacin Jumma’a na garin, inda a ciki ya yi kira ga sauran limamai da malamai da za su gudanar da tafsirai a wannan wata mai kamawa, su kiyaye irin kalaman da za su riƙa yi waɗanda za su iya kawo rashin fahimtar juna tsakanin Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba. Sannan ya nemi malaman su mayar da hankali wajen kira ga haɗin kai da zaman lafiya, domin kyautata zaman tare da fahimtar juna.
Ya ce, idan ma akwai wasu abubuwa na saɓani da ake gani, saboda bambancin aƙida, wanda ya shafi Musulmi ne zalla to, ba a zaurukan sada zumunta, ko wuraren tafsirai za a tattauna su ba. Akwai shugabanni da majalisosi na ilimi da za a iya zama a tattauna su, amma bai dace musulmi su riƙa fitowa bainar jama’a suna sukar junansu da gwara kan mabiya ba, wanda hakan na iya kawo rabuwar kan Musulmi da rashin jituwa.
Shekaru 32 kenan ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Iƙamatus Sunnah mai hedkwata a Jos take gudanar da bita ga malamai, limamai da alarammomi daga ciki da wajen Nijeriya, domin faɗakar da su ƙa’idojin yin tafsiri da sharuɗɗan zama mai gabatar da tafsiri. Domin hakan ya zama manuniya kuma horo ga malaman da za a tura tafsiran a masallatai daban-daban da ke ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar. Wannan yana taimakawa wajen tsaftace yadda tsarin tafsirin ke gudana, da kuma bai wa malaman damar isar da muhimman saƙonni ga al’umma.
A bana wannan ƙungiya ta ba da horo ga malamai, alarammomi da limamai game da amfanin zaurukan sada zumunta da illolinsu. An kuma koyar da su ƙa’idojin yin tafsirin Alƙur’anin Mai Girma, ƙa’idojin gasar karatun Alkur’ani, shugabanci da muhimmancinsa ga Musulmi, da kuma muhimmancin tsoron Allah ga musulmi.
Shirya irin wannan bita da ake yi duk shekara ba ƙaramin amfani yake da shi ba wajen saita hankulan malaman, domin ya tunatar da su abubuwan da suka kamata a riƙa la’akari da su wajen wa’azozinsu da tafsiransu. Hakan harwayau, zai ƙara taimakawa jama’a samun natsuwa da fahimtar tarbiyyar da malamai ke ɗora su a kai cikin watan azumi. Wannan wata ne na ibada, kuma wata mai tsarki da bai kamata a samu wani saɓani ko rashin jin daɗi a cikinsa ba.
Da fatan za mu shiga cikin watan Ramadan cikin masu cikakken imani da lafiya, domin kiyaye ƙa’idojin azumi da sharuɗɗansa. Sannan mu mayar da hankali wajen addu’o’i garemu da iyalanmu da kuma ƙasarmu, don mu samu zaman lafiya, ƙaruwar arziƙi da sauƙin rayuwa.
