Duk marubucin zube zai iya rubuta fim – Zubairu Balannaji

Spread the love

“Rubutu baiwa ne, ba a yi masa ci-da-ƙarfi”

Daga AISHA ASAS

Sanannen matashin marubuci da duniyar rubutu ta ba shi aron lokaci tare kuma da mallaka masa damar yawo cikin lungu da saƙon da ke cikin ta, kasancewar sa ba kawai marubucin zube ba har ma na finafinai. Zubairu M. Balannaji, haziƙin marubuci ne da ke cikin zaratan marubuta da ke ƙoƙarin ganin sun ciyar da harkar rubutu kai har ma ta finafinai gaba. Mai karatu zai amince da zance na ne idan ya yi duba da littafansa da suke kewaye a gidajen ma’abuta karatu tare kuma da shahararren fim da ya shirya wanda yanzu haka ake haska sa a tashar sa ta YouTube wato ‘Kan Ta Qile. A tattaunawarsa da Manhaja, ya zaga da mu cikin ƙoramar rayuwarsa, har muka yi nutso, muka tavo inda muke da tabbacin zai amfani mai karatu. Idan kun shirya, a sha karatu lafiya:

MANHAJA: Mu fara da jin tarihin baƙon na mu.
ZUBAIRU M. BALANNAJI: Assalamu Alaikum Warahamatullahi Wabarakatuhu. Sunana Zubairu M. Balannaji. An haife ni a garin Kano, na tashi a Kano. Na fara karatuna na ‘Nursery’ a ‘Fedwa nursery International School’ da ke cikin F.C.E Kano, daga nan na wuce ‘Demonstration Primary School’ ita ma a cikin F.C.E. Bayan na kammala sai na koma F.C.E ‘Staff Secondary school’ inda na yi karatuna na ‘secondary’. Daga nan kuma na qara komawa F.C.E din dai inda na yi karatun N.C.E program. Na karanci fannin harshe, wato Hausa da Turanci (English/Hausa). Na kammala a shekarar 2014/2015. A yanzu haka ina nan zaune a Kano, inda na ke gudanar da al’amuran kasuwancina da kuma sauran al’amuran rayuwa.

Wanne ɓangare na rubutu kake da wurin zama?
Ɓangaren rubutu da a ka fi sanina a kai, shi ne, na rubutun zube da kuma na wasan kwaikwayo,wato fannin littafan Hausa da kuma tsara rubutun Fina-finai (Scripts writing). Amma baya waɗannan fannonin ma ina rubuta waƙa da kuma rerawa, sai dai a nan fannin ba a san ni yadda ya kamata ba.

Me ya bambanta rubutun zube da na fim?
Abubuwan da su ka bambanta rubutun zube da kuma fim ba su da yawa. Na farko dai shi zube ya na da zaɓi da yawa da mutum zai iya zaɓar wanda ya yi masa ya yi amfani da shi yayin rubutu, misali; idan mutum ya ga dama zai iya amfani da tsarin babi-babi ko kuma ya yi amfani da lambobi, ko kuma Kan batu, idan ya ga dama ma yana iya zuba rubutunsa ratata yadda ya so, ba tare da bin kowanne daga cikin waɗannan tsare-tsaren ba. Yayin da shi kuma fim ba zai tava rubutuwa ya tsaru a haka ba. Dole ne sai ka bi qa’idojinsa daki-daki, matuƙar ka na so ya amsa sunansa na ‘script’ ba wai baragada ba. Rubutun ‘script’ ya na da ƙa’idoji da su ka haɗar da fitowa-fitowa, amfani da manunin lokaci, wanda shi zai nunawa Darakta da Furodusa lokacin da a ke buƙatar ɗaukar fim ɗin, shin da rana ne ko da dare ko kuma da safiya. Akwai bambancewa tsakanin aiki da kuma magana. Sannan akwai bayanin scene ɗin da za a ɗauka ciki ne (Interior) ko kuma waje ne (Exterior) da kuma sauran ƙa’idojinsa.

A cikin su wanne ya fi wuya?
Rubutun littafi a gaskiya ya fi wuya. Shi fim wuyarsa kawai ka san ƙa’idojinsa, shikenan ka gama da shi.

Shin kowanne marubucin zube zai iya rubutun fim?
Sosai ma. Kowanne Marubucin zube zai iya rubutun fim matuƙar ya saka kan sa. Na faɗa miki shi rubutun fim wuyarsa kawai ka san ƙa’idojinsa, sai zama shi ne abu mafi cin rai. Zama kuma wannan dama marubucin zube ai ya saba da shi idan da sabo.

A wacce shekara ka fara rubutu?
Na fara jagwalgwala rubutu a shekarar 2003, amma cikakken rubutuna dai na yi shi ne a shekarar 2006, na kuma buga shi ya shiga kasuwa a farkon shekarar 2008.

Ko za ka iya kai masu karatunmu ga labarin yadda ka fitar da littafinka na farko?
To, yadda na buga littafina na farko dai shi ne; kamar yadda na faɗa a baya, na fara rubutu ne tun a shekarar 2003, amma a lokacin ba wai na ɗauki abin da wani muhimmanci ba ne, kawai dai ina rubutawa ne sai na ba wa Abokaina su karanta, tun a farko ba su yarda ni na rubuta ba, saboda sun ce ba zan iya tsara kamar wannan rubutun da ƙwaƙwalwata na rubuta ba, har dai suka amince ni ɗin ne na ke rubutawa da kaina, sai su ka dawo yaba min idan na ba su sun karanta. A haka dai wani littafin ya vata, wani ya yage saboda karɓa-karɓar da su ke yi da shi a tsakaninsu, wannan ya karanta, idan ya gama ya miƙa shi ga wannan. To, a na ta tafiya a haka dai, har zuwa shekarar 2006, lokacin na rubuta littafina mai suna ‘Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara’, sai na ji ina sha’awar buga shi a matsayin littafi. Sai na samu Mahaifina na faɗa masa. Ya ce to shikenan akwai wani da ya sani a wajen aikinsu yana aikin ɗab’in littafai, zai tuntuɓe shi sai ya haɗa ni da shi mu yi magana. Haka kuwa a ka yi, ya haɗa ni da shi mu ka yi magana, shi Mahaifin na wa ya biya kuɗin aikin ɗab’in a ka buga min, na kai shi kasuwa.

A wannan zamani da alƙaluman rubutu suka fi rinjaye a hannun mata, ko hakan na kawo tangarɗar a kasuwancin naka littafan?
Gaskiya ni rinjayen alƙaluman rubutu a hannun mata bai taɓa shafar kasuwancin littafaina ba. Saboda ina da babban marketer a hannuna, wato Nasir Garba Muhammad (GBS Bookshop), wanda shi ne ya fi kowanne ɗankasuwar littafi sayar da littafan maza tun tali-tali. Ya na da tsofaffin kwastomomi a ciki da wajen ƙasar nan. Don haka iya Nijar kaɗai ma da yankin su Adamawa da maƙotansu za ki yi mamakin adadin kwafin littafai na da su ke sayarwa. Ko da a ke ta kururuwar cewa alƙaluman rubutu sun fi rinjaye a hannun mata a yanzu, to ni na wa ɓangaren mata da yawa ma na fi su buga kwafin littafi mai yawa. Sai dai a yanzu da duniyar rubutu ta shiga tsilla-tsilla ba iya marubuta maza kasuwar ta ke ba wa kashi ba, hatta su kan su matan a yanzu ta kan su su ke yi. Amma ni kam babu abinda zan iya cewa, sai dai na yi godiya ga Allah, tun da har yanzu muna bugawa kuma a na saye daidai gwargwado, duk da dai cinikin bai kai na baya yawa ba, amma muna samun albarka a ciki.

A fahimtarka, me ya sa aka fi son karanta rubutun mata fiye da na maza?
Dalilai guda biyu zuwa uku ne suka sanya a ka fi karanta littafan mata, musamman ma a jihohin da mu ka fi yawan marubuta, irin su Kano, Katsina, Kaduna da sauransu. Amma kamar ni da na ke iya sayar da kwafin littafai na masu tarin yawa a jihohi irin su Adamawa, Taraba da sauransu, da kuma jamhuriyar Nijar da maƙotansu kin ga rashin ciniki mai yawa a jihohin kusa ai ba zai dame ni ba.

Dalilin farko da ya haddasa hakan shi ne,; kasancewar mafi yawan makarantan littafan mata ne, abin ya zama kamar ƙabilanci kwatankwacin na kalmar ciwon ‘ya mace da mafi yawan mata suke amfani da ita. Duk da dai a hakan ma zan iya cewa kusan kaso 35 zuwa 40 na littafan wasu matan marubuta maza ne suke rubuta shi a na yin ungulu da kan zabo a sanya sunan matan. Kin ga an gudu ba a tsira ba kenan! (Dariya). Dalili na biyu kuma shi ne, lokaci, ka san shi zamani wucewa yake yi wani na maye gurbin shi. A baya, musamman ma a zubin farko-farko na marubuta, an yi zamanin da mazan ne zalla suka dinga jan zarensu yadda suke so, yayin da ƙalilan ɗin matan da suke cikin harkar ko motsinsu ba a ji bare amonsu.

Don haka a yanzu zamanin ne ya juya ya koma hannunsu, su ma ya kamata su ja zarensu yadda suke so. Sai dalili na uku shi ne; yadda marubuta maza yawanci mu ke da damar yin rubutu a lokacin ƙuruciya kafin hidimomin rayuwa su yawaita a kanmu. Akwai marubuta maza da yawa da ko da a yanzu idan za su saki sababbin littafai sai an yi mamakin irin yadda za a yi rububin sayensu. Amma sha’anin yau da gobe ya sanya sun bar rubutun ba wai don ba da son sa ba.
 
Idan mun koma ɓangaren rubutun fim, zuwa yanzu ka rubuta finafinai nawa?
Ya zuwa yanzu dai na rubuta fina-finai a ƙalla guda 30 zuwa 35.
 
Wanne ne ya fito a yanzu kuma me ya ƙunsa?
Kusan dukkaninsu sun fito ai, wasu daga cikinsu ma an manta da cewa sun fita, saboda tsawon lokacin da a ka ɗauka da fitar su. Akwai ‘Sakayya’, ‘Alƙawarin Zuci’, ‘Zafin Kishi’, ‘A Sanadin So’, ‘Bayan Badala’, ‘Wasiyya’, ‘Ranar Wanka’, ‘Maimuna Ganɗama’ da sauransu. Sai kuma wanda mu ke tsaka da haska shi yanzu haka, wanda ni ne na rubuta, na kuma shirya shi, mai suna ‘Kan Ta Kile’, a tashar mu ta KUNDIN BAHAUSHIYA TV da ke manhajar YouTube.

Wasu na ganin rubutu baiwa ne kawai yayin da wasu ke ganin za a iya koya a iya. Shin a na ka mahanga ya abin yake?
Gaskiya rubutu baiwa ne. Duk abinda ya kasance baiwa kuwa babu mai iya koya wa wanda ba shi da baiwarsa, komai ƙwarewarsa kuwa, shi rubutu ba a yi masa ci da ƙarfi. Saboda abu ne da Allah Ya ke kimsawa wanda ya so a cikin ƙwaƙwalwa. Don haka ba a iya koyar da rubutu, sai dai a na iya koyar da dabarun inganta shi da kuma ƙa’idoji da alamomin rubutu ga wanda Allah Ya bai wa baiwar yin shi.

A cikin ɓangarorin biyu ko mu ce uku na rubutu da ka ƙware kan su, wanne ne kafi so da sha’awar yin sa?
A gaskiya na fi son rubutun littafi nesa ba kusa ba, saboda shi na fara yi, kuma shi ne ya ƙyanƙyasar da sha’awar rubutun fim ɗin ma gare ni. Ko da littafan da na rubuta na fi alfahari da su fiye da fina-finan da na rubuta. Duk littafin da na rubuta ma ba na taɓa mantawa da shi. Amma ɓangaren rubutun fim ko a kwanakin baya na je gidan wata ‘yar’uwata, muna tsaka da kallo tashar su ka sako wani fim da na rubuta, sai da na ga sunan fim ɗin sannan ma na tuna cewa ni ne na rubuta shi.

Mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.

By Editor