Daga BASHIR ISAH
Gwamnatin Tarayya ta bayyana Litinin, 11 da Talata, 12 ga Yuli, 2022 a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Babbar Sallah.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin Gwamnatin Tarayya a ranar Alhamis, mai dauke da sa hannun Babban Sakataren ma’aikatar, Shuaib Belgore.
“Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin 11 da kuma Talata 12 ga Yuli Julin 2022, a matsayin ranakun hutu don gudanar da bukukuwan Babbar Sallah,” kamar yadda ma’a’ikatar ta wallafa a shafinta na Tiwita.
A ranar Asabar mai zuwa ake sa ran al’ummar Musulmin duniya za su gudana da Idil Kabir na bana.
Biki ne wanda akan gudanar don nuna muhimmancin biyayya da sadaukarwar da Annabi Ibrahim (AS) ya nuna a lokacin da Allah Ya umarce shi da ya yanka dansa Isma’il wanda daga bisani aka maye gurbinsa da rago.
Bikin Babbar Sallah biki ne da aka saba ganin Musulmin duniya kan aiwatar da layya ta hanyar yanka dabbobin da suka sawaka gare su.
