
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya miƙa gaisuwar taya murna ga Kiristoci a jihar da ma Nijeriya baki ɗaya yayin da suke bikin zagayowar lokacin Easter.
Ya yaba masu bisa cika kwanaki 40 na sadaukarwa da addu’o’i, inda ya ce hakan zai taimaka wajen cin nasara ga ayyukan Gwmantin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bila Tinubu.
A saƙon da Kakakinsa, Ohiare Micheal ya fitar a ranar Asabar, Bello ya bayyana muhimmancin lokacin ga al’ummar wanda ya ce hakan wani nau’i ne na ƙarfafa koyarwar addini da al’adunsu.
Ya kuma kiraye su da su cigaba da bai wa Gwmantin Usman Ododo a jihar goyon baya don ganin ta cimma nasarori a yayin aiwatar da ayyukan ci-gaba ga al’umma.
Kazalika, ya yi fatan samun kariya daga Ubangiji gami da kira a gare su da su haɗa kai wajen taimaka wa ci-gaba a kowane ɓangare na harkokinsu.
