Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya buƙaci ‘yan siyasa da sauran al’ummar Kano da su guji duk wani abu da zai janyo rarrabuwar kai ko rikici a jihar. Ya bayyana hakan ne a yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Galadiman Kano, Abbas Sanusi.
A jawabin nasa, Shettima ya ce Kano jiha ce mai tarihin arziki da tasiri a Arewacin Najeriya, kuma ya kamata a kula da zaman lafiyarta. Ya tunatar da yadda rashin zaman lafiya ya ɗaiɗaita wasu manyan birane, yana mai cewa “da zarar an rasa zaman lafiya, komai yana taɓarɓarewa.”
Ya ci gaba da cewa Kano na da matsayi na musamman, inda ya ce: “Idan kana son zuwa Bauchi, Borno, ko Sokoto, dole ne ka bi ta Kano. Jigawa ma kamar ƙarin Kano ce.” Ya roƙi shugabannin siyasa da su saka Kano a gaba maimakon siyasar jam’iyya.
Daga ƙarshe, Shettima ya buƙaci gafara da sasanci tsakanin juna, yana mai cewa “Ku gafarta wa juna. Ina roƙon ku da sunan Allah, kada mu bari siyasa ta raba mu.” Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya raka Shettima a ziyarar ta’aziyyar da ta shafi masarautar Kano.
