Daga UMAR GARBA a Katsina
Wata matashiya mai suna Hauwa’u Lawal Sulaiman ta bayyana yadda jami’an hukumar Hisba ta Katsina suka ci zarafinta, Hauwa ta yi zargin cewa jami’an Hisba sun ci zarafinta bayan wata hatsaniya tsakaninta da babban jami’in kula da ayyuka na hukumar mai suna Mallam Nafiu a hedikwatar hukumar dake birnin Katsina.
Matashiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 15 ga watan Afrilu, a wani filin wasan ƙwallon ƙafa da ake kira Scorpion Arena.
Cikin wata hira da Hauwa Sulaiman ta yi da DCL Hausa a ranar Asabar 19, ga watan April, wadda jaridar Blueprint Manhaja ta bibiya, matashiyar ta bayyana cewa ta kai kayan sana’ar ta a wurin ne, duba da cewa ana gudanar da bikin baje kolin sana’o’i wato ‘Fun fair’.
Sai dai misalin ƙarfe 9 na dare a dai dai lokacin da take ƙoƙarin haɗa kayan sana’ar ta ita da ƙannenta don komawa gida, sai ga jami’an hisba sun yi dirar mikiya a wurin, nan take suka kama ƙannenta maza biyu suka tafi da su ofishinsu.
Lamarin ya ƙazance a lokacin da Hauwa’u da sauran ‘yan uwanta tare da rakiyar wani ɗan sanda suka isa ofishin hisba don yin belin ƙannen na ta.
Hayaniya ta ɓarke tsakaninta da OC operation na hukumar wato Mallam.
“Ya zagi mahaifiya ta na ce masa kada ya sake zagin mahaifiya ta, koda ya sake zaginta ni ma na sai na rama, sai kawai ya mare ni, nima na rama mari na, ban san shine OC operation ba In ji ta”.
Sai dai yaran babban jami’in hisban sun fusata ganin ta mari ogansu, a cewarta akwai ‘yan hisba kimanin mutun ashirin a ofishin a lokacin da lamarin ya faru kuma kowa sai da ya mare ta, a yayin da wasu suka rinƙa dukanta da gora.
“Sun ja ni cikin ofis kuma suka ci gaba da mari na kusan su 20 ɗaya bayan ɗaya suka rinƙa mari na har sai da na rasa ji na.
“Lokacin da suka saka ni cikin cell, akwai wasu mata a ciki, suma sai aka basu umarni su ci gaba da bugu na haka taru suka yi mani dukan tsiya,” in ji ta.
Yanzu haka dai matashiyar da ke neman a bi mata haƙƙinta game da wannan cin zarafi, ta yi ikirarin cewa ta samu karaya a ƙafa da kuma tsinkewar dodon kunne, wanda ya haifar mata da matsalar rashin ji.
Sai dai daga baya an sake ta tare da ‘yan uwanta da aka tsare, bayan wani babban jami’in Hisbah ya shiga tsakani.
Matashiyar ta ce bayan an sake ta, ta je asibiti domin ganin likita.
“Likitan ya ce membrane na kunnena ya tsage akwai buƙatar sai an min tiyata, wannan ɗaurin na ƙafa ta kuma gyaran karayar da suka min ce”. In ji ta
Da majiyarmu ta tuntuɓi hukumar hisba game da zargin, mataimakin kwamanda Mallam Muhammad Shu’aibu, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya musanta wasu zarge zargen, inda ya ce, an sanar da hisba game da bajen kolin amma an sava ƙa’idar abubuwan da aka sanar da hukumar cewa za a yi a wurin tun farko.
A cewar shi an sanar da su cewa ana kaɗe – kaɗen DJ a wurin bajen kolin, hukumar kuma na hani da irin wannan rashin tarbiyya lamarin da ya tilasta shi tura jami’an su don daƙile abunda ke faruwa.
“Ko da jami’an suka je wurin sai aka riƙa jifarsu, a yayin da shi kuma ƙanen wannan matar ya ke ga ya wa hisba cewa basu iya aiki ba, kuma ya yi ƙaryar cewa shi soja ne”.
Lamarin dai ya janyo cece-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda wasu suka yi kira da a gudanar da bincike na gaskiya don yi wa kowane ɓangare adalci.
