Edo 2024: Bishop Kukah ya kare PDP bisa ƙin saka hannu a yarjejeniyar zaman lafiya

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babban limamin cocin Katolika na Sakkwato, Bishop Matthew Kukah, ya ce, babu wanda zai iya tilasta wa jam’iyyar PDP reshen jihar Edo sanya hannu kan duk wata yarjejeniyar zaman lafiya da za a yi a zaɓen gwamna da za a gudanar a ranar 21 ga watan Satumba, inda ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bai sanya hannu ba lokacin da ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023.

An rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya na kwamitin zaman lafiya na ƙasa ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Nijeriya, Janar Abdulsalam Abubakar don gujewa tashe-tashen hankula a lokacin zaɓe.

Jam’iyyar PDP ta yi watsi da yarjejeniyar zaman lafiya kafin zaɓen, wanda ya zama al’adar zaɓe a cikin shekaru goma da suka gabata.

Sai dai kuma da yake magana game da lamarin da aka samu a ranar Lahadin da ta gabata, yayin shirin tsaro na zaɓen Edo a birnin Benin, Bishop Kukah wanda yana ɗaya daga cikin masu kiran kwamitin zaman lafiya na ƙasa, ya ce ƙungiyar ba za ta iya tilasta wa kowane ɗan takara sanya hannu ba.

Yayin da yake magana a kan yadda ake cewa rashin sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya da jam’iyyar PDP ta yi ba daidai ba ne, Kukah ya bayyana cewa shugaban ƙasa na yanzu Bola Tinubu shi ma ya ƙi sanya hannu a lokacin yana ɗan takarar shugaban ƙasa.

“Kwamitin zaman lafiya na ƙasa, abin da muke yi ba ya cikin dokar zaɓe, ba doka ba ne. Kawai kai halin kirki ne. Ba za ku iya tilasta wa mutane su so abokan hamayya ba.

“Idan ka koma zaɓen 2015, Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, bai zo ya sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ba. Kuma ‘yan adawa sun je wurin, abin da ya kamata ya kasance, sai washegari Atiku ya zo ya sa hannu.

“Haka zalika, wani abin sha’awa shi ne, shugaban ƙasar na yanzu bai sanya hannu ba a lokacin da yake ɗan takarar shugaban ƙasa, wanda hakan ya nuna cewa hakan ba laifinmu ba ne ‘yan adawar siyasa su yi amfani da shi.

“Abin takaici ne amma ba za mu gurfanar da kowa a kotu ba saboda rashin sa hannu a kan sa. Abin da kawai yake yi maka a matsayinka na dan takara shi ne ya aika da saƙon da bai dace ba wanda ‘yan adawa za su iya amfani da su,” in ji Kukah.

A watan Satumban 2022, tsohon gwamnan Legas kuma ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a 2023, Bola Tinubu, bai sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan takararsa suka ƙulla ba. Abokin takarar sa a lokacin kuma tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ne ya wakilce shi a wajen taron.

By ukarofi