EFCC ta kama mutum 20 bisa zargin laifukan zaɓe a Abuja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hukumar EFCC ta sanar da kama mutum 20 da ake zargi da aikata laifukan zaɓe yayin zaɓen ƙananan hukumomin babban birnin tarayya, Abuja da aka gudanar a ranar 21 ga Fabrairu, 2026.

Ta ce an kama su ne a wurare daban daban saboda zarge zargen sayen ƙuri’u da sayar da ƙuri’u da kuma hana jami’ai aiki, inda aka gano kuɗi har Naira miliyan 17,218,700.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale, ya fitar, an ce an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin da Naira miliyan 13,500,000 a cikin mota da aka ajiye kusa da rumfar zaɓe a yankin Kwali.

Sanarwar ta ƙara da cewa an kama mutane biyu a Abaji, tara a Gwagwalada, huɗu a Kuje, sannan sauran huɗun a Kwali.

Hukumar ta ce za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.

Hukumar INEC ce ta gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a dukkan yankuna shida na FCT.

Haka kuma an gudanar da zaɓukan cike gurbi a mazaɓun Ahoada East II da Khana II na Jihar Ribas.

An kuma gudanar da zaɓe a mazaɓun Kano Municipal da Ungogo na Jihar Kano.

EFCC ta jaddada cewa za ta ci gaba da sa ido domin tabbatar da gaskiya da adalci a dukkan matakan zaɓe.

By ukarofi