
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya shiga hannun jami’an Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, bisa zargin sa da hannu a badaƙalar wasu tsabar kuɗaɗe da adadinsu ya kai Naira biliyan 189.
Tambuwal, wanda tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ne, ya kai kansa hedikwatar EFCC a Abuja da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar ranar Litinin, inda masu bincike suka yi masa wasu tambayoyi.
Wani jami’i da ya nemi a sakaye sunansa, ya shaida wa jaridar Vanguard cewa ana zargin tsohon gwamnan ne da fitar da wasu kuɗaɗen al’umma a zamanin mulkinsa a jiharsa ba tare da bin tsarin doka ba.
Ya kuma ce, tsawon watanni kenan anan gudanar da bincike akan al’amarin.
Kawo yanzu EFCC ba ta fitar da wani jawabi na musamman a kai ba.
Tambuwal, wanda jigo ne a jam’iyyar PDP, ya yi gwamna a Sakkwato Daga 2015 zuwa 2023, haka kuma ya taɓa riƙe muƙamin Kakakin Majalisar Wakilai.
A halin yanzu sanata ne shi a majalisa ta 10, inda ya ke wakiltar mazaɓar Sakkwato ta Kudu.
