Kaduna: Zanga-zanga ta ɓarke bayan jami’an NDLEA sun harbe na gefen hanya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A jiya Litinin al’umma a yankin Barnawa da ke Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu suka shiga mawuyacin hali bayan zargin wasu jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) sun harbe wani matashi.

Lamarin da ya haifar da zanga-zanga daga wasu fusatattu tare da cika tituna da rufe wani sanannen wajen shaƙatawa.

Wani shaida ya ce, wanda aka harben ya kasance mutum ne kamili kuma jajirtacce wajen nema abincinsa, inda wani alburushi ya same shi bisa kure a yayin da jami’an suke farautar wani dillalin ƙwaya.

Al’amarin ya auku ne a yankin madakatar motoci ta kasuwar Barnawa, inda waje ne da ya shahara da tara jama’a a lokacin dare.

Wani mai suna Musa ya shaida wa manema labarai cewa jami’an sun biyo sawun wani mutum ne da ake zargin yana ɗauke da kayan maye, inda suka je yankin a wata mota ta gida.

Akan haka ne masu shaguna da wuraren cin abinci suka rufe wuraren kasuwancinsu don ƙauce wa asara.

By Babaji