An kama sojojin Mali bisa zargin yunƙurin juyin mulki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rahotanni daga Bamako, Babban Birnin ƙasar Mali sun ce an kama sojoji da dama bisa zargin su da shirin kifar da mulkin sojin ƙasar.

An yi kamen ne a dare ɗaya wanda kuma ake sa rana cigaba da yi a yayin da jagorancin ƙasar ke fuskantar matsi sakamakon rahotannin ƙamarin rashin tsaro daga arewacin ƙasar.

Kawo yanzu hukumomin ƙasar ba su yi tsokaci game da kamen ba.

Wani rahoto da BBC ta fitar ya nuna cewa, da fari Janar Abass Dambele, wanda tsohon gwamnan shiyyar Mopti ne da Janar Nema Sagara, ɗaya daga cikin manyan sojoji mata a ƙasar, suna daga cikin waɗanda aka tsare.

Saidai, wani makusancin Janar Dambele ya shaida wa BBC’n cewa babu ɗaya daga cikinsu da aka kama.

Rahoton kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana cewa, ana zargin sojojin da aka tsare da shirin kifar da gwamnatin kamar yadda majiyoyi da dama suka shaida.

Wata majiya ta ce, an kama aƙalla sojoji 50 waɗanda manufarsu ita ce kifar da gwamnatin domin hargitsa al’amura a hukumomin ƙasar.

By Babaji