EFFC na neman majalisa ta amince da dokar bincika arzikin ‘yan Nijeriya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci a Nijeriya Ola Olukayode ya shawarci majalisar tarayyar ƙasar ta amince da ƙudirin dokar “Uneɗplained Wealth Bill”, wanda zai ba ta damar bincikar ɗaiɗaikun ‘yan Nijeriya game da yadda suka tara dukiyarsu.

Olukayode ya ce ƙudirin ya je gaban ‘yanmajalisar tun a majalisa ta tara, wanda suka yi watsi da shi, kamar yadda kamfanin labarai na NAN ya ruwaito.

“Akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin ɓarnar da ake yi arzikin ƙasarmu da kuma matsalar tsaro,” a cewarsa yayin wani taro da kwamatocin majalisar tarayya suka shirya kan arzikin ƙasa.

“Idan kana binickar ayyukan ‘yan fashin daji, da ta’addanci, za ka ga suna da alaƙa da wani nau’i na cin hanci da rashawa, ko kuma karkatar da kuɗaɗen da suka kamata a yi wa al’umma aiki.

“Ina neman ku taimaka min wajen amincewa da ƙudirin Uneɗplained Wealth Bill. Shekara ɗaya kenan ina neman hakan, kuma shi ne dai majalisa ta tara ta yi watsi da shi. “Idan ba mu binciki dukiyar da mutane suka tara ba ba za mu taɓa gyara al’amuran ba.

“Akwai wani da ya yi aiki shekara a wata ma’aikata. Mun lissafa baki ɗayan albashi da alawus ɗinsa. Sai kuma muka gano gidaje biyar da yake da su, biyu a Maitama, uku a Asokoro. Amma kuma ana so mu gabatar wa kotu hujja a kansa kafin mu yi wani bincike. Wannan abin takaici ne.”

By ukarofi