Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, ya yi kakkausar suka ga zargin da ake masa na cewa yana da alaƙa da gwamnatin Janar Sani Abacha, tsohon shugaban mulkin sojan Nijeriya.
A cikin wani cikakken bayani da ya wallafa a shafinsa na ɗ da aka fi sani da Tiwita a ranar Laraba, Obi ya yi tsokaci game da zargin haɗa baki da gwamnatin Abacha, wadda ta mulki Nijeriya daga 1993 zuwa 1998.
Domin nuna goyon bayansa ga matsayinsa da kuma kawar da jita-jitar da ake yi, Obi ya fitar da wata wasiƙar naɗi a gwamnatin tarayya daga 1996, inda ya nuna cewa an haɗa shi da kwamitin gwamnati na yaƙi da cunkoson ababen hawa, wani shiri da aka yi niyya don magance gazawar da ta addabi ayyukan tashar ruwan Nijeriya a lokacin.
Da yake nanata matsayinsa a yayin wata hira da aka yi da shi kwanan nan, Obi ya dage cewa bai taɓa haɗuwa da Abacha ba, duk da cewa yana aiki a kwamitin fasaha da aka kafa a zamanin marigayin.
“A bisa ƙa’idojin da na kafa na kare duk wani abu da nake da hannu a ciki, da kuma maslahar dukkan maza da mata masu son zuciya, musamman waɗanda suka jajirce wajen neman gaskiya, na haɗa wasiƙar da ke ƙunshe da haɗin gwiwa na, tare da wasu, a cikin aikin kan rage cunkoso a tashoshin jiragen ruwa,” Obi ya rubuta.
Ya jaddada cewa rawar da yake takawa ta zaman kanta ce ta al’umma da tattalin arziki, ba ta siyasa ko aƙida ba, kuma ya zo ne a matsayin mayar da martani ga yadda ƙasar nan ke ci gaba da fuskantar cikas na hada-hadar kayayyaki da kasuwanci a manyan tashoshin jiragen ruwa. A cewarsa, wannan yarjejeniya wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ƙasa ke yi na bunƙasa kasuwanci da kuma kawar da tarnaƙi a harkokin shigo da kayayyaki.
Obi ya fayyace cewa shigarsa a wannan aiki ba naɗin siyasa ba ne illa gudunmuwar ƙwararru tare da wasu masu zaman kansu. Wasiƙar, wacce aka fitar a shekarar 1996, ta yi bayani dalla-dalla maƙasudin aikin rundunar na inganta ingantaccen tashar jiragen ruwa da sauƙaƙa tafiyar da harkokin kasuwanci cikin sauƙi, aikin da ya ce ya yi dai-dai da muhimman ɗabi’unsa na sake fasalin tattalin arziki da hidima.
Ya ƙara da cewa, “An bayar da wannan bayanin ne domin tabbatar da gaskiya, don tabbatar da cewa ayyukanmu sun gudana ne kawai ta hanyar jin daɗin jama’a ba burin siyasa ba,” inji shi.
Tsohon mai fatan zama shugaban ƙasar ya kuma zargi masu sukar da gangan da karkatar da labarin don cimma wata manufa ta siyasa, yana mai bayyana su a matsayin “masu aikata ɓarna da mugun nufi.”
Obi ya ƙara da cewa, ya fitar da wasiƙar ne ba wai don ya gamsar da masu zaginsa ba, sai dai don ya daidaita tarihin zuriya da kuma masu son gaskiya.
“Ba na tsammanin wannan ƙwaƙƙwarar shaida za ta binne wannan shari’ar ta Abacha saboda masu yin ɓarna na da wata manufa ta ɓoye, amma ana sanya ta ne a fili domin ‘yan baya da kuma bayyana gaskiya da alƙawarin da na yi wa ‘yan Nijeriya kan duk wani batu da na shiga,” inji shi.
Ana kallon martanin Obi a matsayin wani yunƙuri na kiyaye mutuncin siyasarsa da kuma ƙarfafa iƙirarinsa na kawo sauyi, musamman a yayin da ake ci gaba da cece-kuce game da makomar siyasarsa a zabukan 2027.
Jigon jam’iyyar Labour ya ci gaba da nuna kansa a matsayin tsaftataccen daga tsarin siyasar Nijeriya, wanda galibi ke fafutukar tabbatar da shugabanci nagari, haɗa kan matasa, da sanin ya kamata.
