Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar hana fasa ƙwauri ta Nijeriya, ta kama wata mota da ke ɗauke da wata kontena maƙare da Mazaƙutar jakai fiye da 10,600.
Hukumar ta kama motar a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Maimagana da yawun hukumar ta Custom, Abdullahi Aliyu Maiwada shaida wa Manhaja cewa an daskarar da mazaƙutar jakunan ne cikin kontena da nufin safararsu zuwa ƙasashen ƙetare.
Abdullahi Maiwada ya ce sun samu nasarar kama sassan jakunan bayan samun bayanan sirrin da suka jima suna tattarawa game da safarar.
Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ake kashe jakuna a Nijeriya, ”wannan yana nuna girman yadda ake kashe waɗannan dabbobi a Nijeriya da makwabtan ƙasashe”.
Maiwada ya ce hakan na barazana ga rayuwar dabbobin, wanda zai iya sanya wa su ƙare a ƙasar idan ba a ɗauki mataki ba.
Kakakin hukumar ya ce ana safarar wasu sassan irin waɗanan dabbobi daga ƙasashen Afirka ta dama tare da kawo su Nijeriya daga nan kuma a kai su ƙasashen waje.
