Elon Musk ya yi asarar Dala biliyan 34 a kwana ɗaya bayan takun-saƙa da Trump

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Matakin arziƙin shahararren Ba’amurken Attajirin nan, wato Elon Musk ya yi ƙasa da kimanin Dala biliyan 34a ranar Alhamis wanda hakan ɗaya ne daga cikin asara mafi girma da ya tafka a tarihin dukiyarsa, kamar yadda Bloomberg Billionaires Index ta bayyana.

Hakan ya biyo bayan takun-saƙa da Shugaba Donald Trump a sakamakon kalaman da Musk, wanda shi ne shugaban kamfanonin Tesla da SpaceX ke wallafawa a shafin X, waɗanda ke nuna ƙiyayyarsa a fili ga Trump da gwamnatinsa.

Daga cikin maganganun Musk akwai wanda ke alaƙanta Trump da Jeffrey Epstein, wanda ya ce Shugaban ƙasar ya taka gagarumar rawa wajen cimma nasara a zaɓen 2024. Zargin da ya sa Trump ya yi barazanar ƙwace kwangilolin gwamnati da aka bai wa kamfanonin Musk.

Shugaba Trump ya kuma yi gargaɗin harajin motar lantarki ta EV da aka samar a gwamnatin Shugaba Joe Biden a shekerar 2022, wanda ta nan ne kwastomomin Tesla suke samun lada har zuwa Dala 7,500 akan kowane ɗaya da aka saya.

A yayin bada amsa ga barazanar Trump ne Musk ya ci alwashin soke tsarin Dragon spacecraft na SpaceX.

By Babaji