Gwamnatin Katsina ta biya Naira miliyan 436 matsayin diyyar aikin hanya a Funtua

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta biya waɗanda aka karɓi filayen su domin aikin tagwayen hanya a Jinkiri zuwa Sokoto road da ke ƙaramar hukumar Funtua.

Kwamishinan ma’aikatan ƙasa da tsare tsare Dr Faisal Umar Kaita ya sanar da haka a lokacin da yake miƙa chajin kuɗin diyyar ga masu filayen da wakana a ɗakin taro na karamar hukumar Funtua.

Kwamishinan wanda ya sami wakilci muƙaddashin babban sakatare na ma’aikatar malam Dikko Bala ya ce idan aka kammala wannan aikin zai kawo bunƙasa a tattalin arzikin yankin da kuma rage cunkoso a hanyar zuwa Sokoto.

A jawabin sa mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Funtua, ya yaba wa gwamna Dikko Raɗɗa kan gina ‘yan tawayen hanyoyi a cikin garin Funtua.

Shima wakilin Hakimi Funtua Alhaji Abubakar Sani Yusuf ya yaba wa gwamnatin jihar bisa biyan kuɗin diyyar tun kafin a fara aikin hanyar da yace wannan shine karo na farko a tarihin Jihar Katsina.

Sai yayi kira ga al’ummar yankin da aikin hanyar ya shafa da suba yan kwangilar haɗin kai wajen ganin sun gudanar da aikin ba tare da wata matsala ba.

By ukarofi