
Emefiele ya samu sa’ida bayan Kotun Ɗaukaka ƙarar ta soke ƙwace wasu kadarorinsa
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kotun Ɗaukaka Ƙara a Legas, ta soke umarnin ƙwace wasu kadarorin tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele da aka miƙa wa Gwamnatin Tarayya.
A watan Nuwamban 2024 ne Babbar Kotun Tarayya a Legas ta yi hukuncin damƙa wa Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) kadarorin Emefiele bisa zargin sa da mallakar su ba bisa doka ba.
Jaridar NewsPoint Nigeria ta ruwaito kadarorin kamar haka; “The forfeited assets included two fully detached duplexes located at No. 17B, Hakeem Odumosu Street, Lekki Phase 1, Lagos; an undeveloped land measuring 1,919.592 square metres with survey plan No. DS/LS.340 at Oyinkan Abayomi Drive (formerly Queens Drive), Ikoyi, Lagos; a bungalow at No. 65A Oyinkan Abayomi Drive, Ikoyi, Lagos and a four-bedroom duplex at No. 12A, Probyn Road, Ikoyi, Lagos.”
Ta kuma wallafa cewa, “Others were – an industrial complex under construction on 22 plots of land in Agbor, Delta State; eight units of uncompleted apartments on a plot measuring 2,457.60 square metres at No. 8A Adekunle Lawal Road, Ikoyi, Lagos and a fully detached duplex on a plot measuring 2,217.87 square metres at No. 2A Bank Road, Ikoyi, Lagos.”
Bugu da ƙari, kotun ta umarci a karɓe Dala 2,045,000 da takardun hannun jari na kamfanin Queensdorf Global Fund Limited da aka miƙa wa Gwamnatin Tarayya.
An yi hukuncin ne bisa jawabin EFCC na cewa, Emefiele ya mallaki kadarorin ne ta hanyar gudanar da wasu haramtattun ayyuka, kamar yadda bai gabatar wa cibiyar bincike takardun bayanan kadarorinsa ba a lokacin da ya ke gwamna.
Saidai, a yayin hukuncin Alƙali Abdulazeez Anka, kotun ta ce ta gamsu cewa kuɗaɗen halaliyar da wanda aka shigar ƙarar ya ke samu, za su iya mallaka masa kadarorin, don haka ne ta tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayyar ta Legas, wanda ta yi a ranar 1 ga watan Nuwamban 2024.
