Gwamnatin Tarayya na shirin cimma matsaya da ofisoshin jakadanci kan kuɗaɗen hayar ƙasa

Spread the love

Gwamnatin Tarayya na shirin cimma matsaya da ofisoshin jakadanci kan kuɗaɗen hayar ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa game da kuɗaɗen hayar ƙasa da ake bin da dama daga cikin ofisoshin jakadanci ƙasashen waje a birnin tarayya Abuja.

A lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai a ranar Lahadi, Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ya ce Hukumar Kula da Birnin Tarayya (FCTA) ce za ta yi aiki game da al’amarin.

Ya kuma ce, za yi amfani ne da hanyar tattaunawa tsakanin hukumar da kuma wakilan ofisoshin jakadancin.

Kakakinta ya bada tabbacin hakan ne biyo bayan samun rahotannin da ke cewa akwai yiwuwar FCTA ta ɗauki matakin doka waje rufe ofisoshin jakadanci guda 34 bisa rashin biyan kuɗaɗen hayar ƙasa tun daga shekarar 2014.

A sanarwar da FCTA ta yi, ta ce kimanin jimillar Naira biliyan 3.6 na kuɗaɗen hayar ake bin ofisoshin bashi.

A baya ne Ministan Abuja, Nyesom Wike ya umarci a rufe kadarori guda 4,800 kan rashin biyan kuɗin haya, inda daga bisani Shugaba Bola Tinubu ya tsoma baki a lamarin tare da sake ba su alfarmar mako biyu domin su kammala biyan bashin da ake bin su.

Daga cikin ofisoshin jakadancin da lamarin ya shafa akwai; “Ghana High Commission Defence Section; Embassy of Thailand, Embassy of Côte d’Ivoire; Embassy of the Russian Federation; Embassy of the Philippines; Royal Netherlands Embassy; Embassy of Turkey, and the Embassy of the Republic of Guinea”, kamar yadda NewsPointNigeria ta ruwaito.

Haka kuma akwai ofisoshin jakadancin Ireland, Uganda, Iraq da The Zambia High Commission.

Sauran sun haɗa da “the Tanzania High Commission, German Embassy, Embassy of the Democratic Republic of Congo, Embassy of the Bolivarian Republic of Venezuela, Embassy of the Republic of Korea, and the High Commission of Trinidad and Tobago.”

Da kuma “The Embassy of Egypt, Embassy of Chad, Sierra Leone Commission, High Commission of India, Embassy of Sudan, Embassy of Niger Republic, and Kenya High Commission and the embassies of Zimbabwe, Ethiopia, and Indonesia”, kamar yadda jaridar ta wallafa.

By Babaji