
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A safiyar ranar Lahadi ne jama’a suka gudanar da zanga-zanga a Birnin Makurɗi dake Jihar Benuwai domin nuna fushinsu game da kisan gilla da aka yi wa mutane 107 a ƙauyen Yelwata dake Ƙaramar Hukumar Guma a jihar kwanan nan.
Masu zanga-zangar waɗanda galibinsu matasa ne, sun tare Shataletalen Wurukum, wanda ya haɗe hanyoyin zuwa Abuja, Gboko, Enugu da Birnin Makurɗi, lamarin da ya jefa masu zirga-zirga cikin matsi.
Masu zanga-zangar sun bayyana kaďuwarsu game da kashe-kashen al’umma da mahara ke yi akai-akai a sassan jihar da rashin magance matsalar daga gwamnatin jihar.
An ga yadda suke ɗauke da alluna da ke ɗauke da rubutun “Enough of the killings in Benue State!”, “We are tired, broken, and helpless”, “The government isn’t helping us”, “The number of deaths is uncountable, and we don’t know where they will strike next”.
A yayin al’amarin, jami’an tsaro sun yi dandazo a yankin da nufi tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Daga bisani duba da zanga-zangar ka iya juyawa zuwa tarzoma, jami’an tsaro sun watsa hayaƙi mai sanya hawaye da yin harbe-harbe a iska, lamarin da ya sa suka watse a inda wasu daga cikinsu suka samu raunuka.
