Ko akwai kurakuren kimiyya a Qur’ani?

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ 

A baya bayan nan Mulhidai, Riddaddu da makiya Musulunci sun shigo da wata sabuwar hanya ta sukar addinin musulunci, musamman a kasashen yamma, ta amfani da cewa akwai tarin kura-kurai na kimiyya a cikinsa. Na sha gwagwarmaya da irin wadannan mutane a dandalin Quora inda na kalubalanci duk wani mai wannan da’awar ya kawo duk wani abu da yake tsammani na kimiyya ne wanda ya ci karo, ko ya sha banban da Qur’ani. Dalili na kuwa bai wuce cewa na yi imani da cewa Allah dai shine wanda ya yi duk wata halitta, kuma a tsari irin na kimiyya ya yi halittunsa, sannan shine wanda ya saukar da Qur’ani, don haka duk wanda ya ce akwai karo daga wadannan bangarori guda biyu, to tabbas bai wuce ko dai ba shi da ilimin Qur’ani yadda ya kamata ba, ko kuma ba shi da ilimin kimiyya cikakke. 

Abokan muhawara ta sun kalubalance ni da kawo tambayoyi guda goma da su ka jibanci kimiyya a Qur’ani wadanda su ka hada da; Faduwar Rana, Samar da maniyya a jikin dan Adam, halittar mutum daga gudan jini, Tsaunuka a matsayin turaku da ke rike kasa, adadin duniya guda nawa, zagayen Rana, Sama a matsayin rumfa, tarihin asalin samuwar halittu, wata a matsayin haske da kuma shinge da ya raba tekuna. To bari mu bisu daya-da-daya.

1. Faɗuwar rana- Sun ƙalubalanci ayar cikin Suratul Kahfi cewa; Q18:86 “Har a lokacin da ya isa mafadar rana, kuma ya same ta ta na bacewa a cikin wani ruwa mai kamar bakar laka.”

Sun ce wannan aya ta yi karo da bayanai na Zahiri da kimiyya ta tabbatar domin ayar na nuna cewa rana na faduwa a nan duniya ne. To wannan ikirari ba daidai ba ne domin idan mu ka duba ayar da farko dai zamu gane cewa tana bada labarin wani mutum guda ne, wato Zulqarnaini na yadda ya ga wannan lamari na faduwar rana ba labarine na kimiyya ba. Labarin da ba na kimiyya ba kuwa, ta yaya za’a yi ya yi karo da kimiyya? Abu na biyu da zamu yi la’akari da shi shine Kalmar mafadar rana ba ta na nufin hakikanin inda rana ke faduwa ba ne. Misali a zamunan baya, yan kasar Japan na kiran China da sunan mafadar rana, saboda itace kasa mafi yamma da su. Haka nan larabawa na kiran kasar Morocco da “Maghrib” wato mafadar rana saboda nan ne kasa mafi yammaci da daular larabawa a wancan lokaci.

Don haka ambaton cewa Zulqarnain ya isa mafadar rana a waccan lokaci ba ya na nufin inda hakika rana ke faduwa ba ne, a’a, shine dai gari mafi yammaci da nisa. Hujja ta uku kuma ita ce, bayanin cewa ranar na bacewa cikin wani ruwa mai kamar bakar laka, ana bada labarin ne daga kwayar idon Zulqarnain. Rana da wata a yayin faduwarsu su na bada launi daban daban sakamakon yadda iska da haske a sararin samaniya ke tasiri wajen yadda mutane ke ganin halittun sammai. Akwai abinda ake kira da pink moon, saboda a yanayin da aka ganshi ya na fitowa da launin pink, shin watan pink ne? Sannan sama da rana,  sai a ga ta yi shudi amma da dare sai aga ta yi baki. To launi a sama ya ta’allaka da kwayoyin iska ne da haske. Don haka Allah na mana bayanin wannan sirri shekaru 1400 tun kafin masana kimiyya su gano tasirin iska da haske wajen launin halittun sammai. Shi yasa aka ce haka Zulqarnain ya ga faduwar ranar a gari mafi yammaci da ya je. Kuma a duk inda kake a doron kasa a lokacin faduwar rana za ka ga ta na nutsewa ne a karshen inda idon ka ke iya Hange, wato horizon.

2. Samar da maniyyi– Bayanin Qur’ani na inda ake samar da maniyya a jikin Dan Adam shi ma ya sami kalubalen cewa ya ci karo da na kimiyya. Allah ya ce a cikin Suratul Darik; Q86:6-7 “An halitta shi daga wani ruwa mai tunkudar juna…ya na fita daga tsakanin tsatso da karankarmar kirji.”

Sai su ka yi wuf su ka ce “Ayya…Qur’ani ya kwafsa a kimiyance a nan, saboda maniyyi daga cikin yayan gwaiwa ake samar da shi”. To ku dan dakata mana. Allah ya yi maganar tsatso ne, wato Kalmar larabci “Sulbi” wadda ke nufin tsatso wadda ita dai Allah ya yi amfani da irinta cikin Suratul Ma’ida a aya ta 23 wato “Aslabikum” wadda ke bayanin cewa “Da matan yayanku wadanda su ke daga tsatsonku” a larabci da turanci Kalmar na nufin “Loins” wato daga kasan kirji zuwa yan maraina. To, menene ya ci karo da kimiyya da ke cewa maniyyi ana samar da shi a maraina?

3. Halitta daga gudan jini– Shi ma wannan bayani na Qur’ani ya gamu da suka. Allah ya ce cikin Suratul Alaq; Q96:2 “Ya halitta mutum daga gudan jini.”

Allah ya kira surar gaba dayanta da “Gudan jini” wato Alaq, kalmar da ba ka iya fahimtarta yadda ya kamata sai ka san tsarin kimiyya na yadda Allah ke halitta mutum a cikin ciki. Kafin kimiyya ta gano yadda tsarin ya ke, har zuwa kusan karni na 18 ana daukar cewa jariri na farawa ne a dan mitsitsi da duk sifofinsa cif, kafin ya girma a hankali ya isa haihuwa. Amma Allah sama da shekaru 1400 ya yi bayanin yadda yanayin ya ke tun daga daukar ciki zuwa haihuwa. Wannan bayani ya zo a warwatse cikin Qur’ani, bari mu biyo shi tun asalinsa. Allah ya fara da gaya mana cikin suratul Yasin cewa: Q36:36 “Tsarki ya tabbata ga wanda ya halitta nau’ika na namiji da mace, dukkansu daga abinda kasa ke tsirarwa, Kuma daga (su) kansu, Kuma daga abinda ba su sani ba.”

Hikimar hakan shine domin Allah ya tabbatarwa dukkan wata halitta buwayarsa cewa shine kadai tilo. Amma duk wata halitta, mai rai ko maras rai ta bi tsarin cewa ta na da kishiya, shi kadai ne ba shi da kishiya. Halitta mara rai dukkanta daga kwayar zarra take (Atom) wanda ke cikin tsarin lantarki mai karbar wuta (+ positive) da mai bada wuta (- negative). Halitta mai rai kuma ko wacce iri, na cikin tsarin kwayar halitta (cell) da ke da sinadarin mace da namiji, hatta halittu masu kwayar halitta daya, Inda namiji ke barbarar ta mace. Akasarin halittu masu rai na samuwa daga wannan tsari na barbarar namiji da mace a daidaikun halittu biyu. Akwai kuma masu kwayar halitta daya wadanda ke da namijin da mace a halitta guda. To, a tsarin halttar mutum sai Allah ya fara da cewa; Q56:58-59 “Shin kun ga abinda kuke fitarwa na maniyyi…shin kume kuka halitta shi ko mune masu halittawa?”

Wato matakin halitta na farko shine daga maniyyi na namiji wanda ke shiga cikin mace bayan saduwa. Daga nan sai Allah ya ce; Q86:6-7 “An halitta shi daga wani ruwa mai tunkudar juna.”

A kowacce fitar maniyyi daga namiji izuwa jikin mace, akwai kwayoyin halittar mutum (spermatozoa) kama daga miliyan 150 zuwa miliyan 200, cikin duk millitre daya ta maniyyi na lafiyayyen mutum. Kowanne daya kuma cikin wadannan miliyoyi 200 zai iya samar da mutum. To wannan dandazon shine fa a jikin mace bayan jima’i, sai su kama tsere da rigegeniyar wanne a cikinsu zai iya fasa kwan macen ya zama shine ango? Wato wannan tsere shi Allah ke nufi a wannan aya da ke cewa “Su na tunkudar juna”. Kwayar maniyyin, an suranta ta yadda jikinta ya zama kanta kewayye ne wanda aka lullube da wani sulke-sulke a goshinsu, sai kuma doguwar jela tamkar yadda zaka ga yayan kwadi bayan kyankyasarsu. Jelar ta su kuma kamar ta maciji, ita ke tunkuda su domin iyo cikin gaggawa. A yayin da su ka isa ga kwan mace, sai su kewaye shi su yi masa kuri su yi amfani da wannan sulke na goshinsu wajen samun nasarar fasa wannan kwai. To duk wanda ya riga fara fasa wannan kwai sai ya shige cikinsa. Kwan mace, shine kwayar halitta (Cell) mafi girma cikin kwayoyin halitta a jikin Dan Adam kuma ya ninninka na maniyyi. Hikimar shine idan maniyyi ya shige cikinsa su ka dunkule, shine mataki na samuwar sabon mutum, mace ko namiji, don haka ya na bukatar wannan girma domin hadiye maniyyi da samar da sinadari domin rayuwar dan tayi a cikin mahaifa. To da zarar gudan maniyyi ya sami zama wannan ango, gaba dayan sauran miliyoyin kwayoyin maniyyin sai su yi saranda su mika wuyar cewa an kasa su. Sai Allah ya ci gaba da bayani a cikin suratul Insan (Mutum); Q76:2: “Lallai ne hakika, mu mun halitta mutum daga wani ruwa garwayayye.”

Kun ji Kalmar da Allah ya fada “Garwaya” wato ya garwaya kwayar maniyyi da kwan mace lokacin da aka daura wannan aure a cikin mace. Sannan kuma da maniyyi da kwai na macen, kowannesu na dauke da kwayoyin halittar gado (Chromosomes) guda 46 kuma tagwaye ne, wato bibbiyu. Amma sakamakon wannan gauraya, sai maniyyi ya yago rabin wadannan kwayoyin halittar gadon nasa, wato guda 23 yayinda kwan mace shi ma sai ya yago nasa rabin, 23 sai su gauraya wadannan rabi-rabin yadda idan su ka dunkule kaga sun sake samar da wasu 46 da kowanne mutum ke dauke da su. Wannan ne ya ke sa ake samun gadon sifa da halayya ta iyaye biyu, mace da namiji a jikin dan su. Bayan wannan gauraya, wane mataki kuma dan tayin zai hau?; Q23:13 “Sannan mu ka sanya shi digon maniyyin a cikin matabbata nutsatstsiya.”

Wannan garwayayyen digon maniyyin (fertilized ovum) sai ya bi wani bututu (fallopian tube) ya shiga mahaifa (Uterus) inda zai je ya makale a jikinta. A nan, dan tayin zai fara rayuwa ya na samun abincin da zai gina jikinsa har zuwa haihuwa. To a nan ne fa shi wannan garwayayyen maniyyi zai fara rabewa, daga daya ya zama biyu, su kuma su zama hudu, hudun su zama takwas, zuwa sha shida, talatin da biyu, haka-haka dai kwayar halittar za ta yi ta ninkawa har sai ya zama daruruwa wanda zai dunkule (blastocyst); Q23:12 “Kuma lallai ne, hakika mun halitta mutum daga wani tsantsa.”

Ya fara zama tsoka ke nan da ke dauke da kwayoyin halitta na asali (stem cell) wadanda ke iya samar da duk wani sassa na halittar mutum. Kamar yadda Allah ya ci gaba da bamu bayani a; Q23:14 “Sannan kuma mu ka halitta shi gudan jini.”

Sai kuma jijiyoyin jini su karade wannan tsoka da ke dauke da kwayoyin halittar na asali (stem cell) da ke dauke da bayanai (information) da zasu iya zama kowane irin kwayar halitta a jikin mutum kamar su jini, tsoka, kashi ko jijiya ko gashi kowannensu. Daga nan kuma sai… Q23:14 “…Sannan muka halitta gudan jinin tsoka, sannan mu ka halitta tsokar ta zama kasusuwa, sannan muka tufatar da kasusuwan da wani nama (fata).” 

Abu na gaba mahimmi a dan tayin shine banbance yadda halittar za ta zama, wato mace ko namiji? Sai Allah ya ce mana; Q92:3 “Da sirrin da ya halitta namiji da mace.”

Wato a cikin kwayoyin halittar gado da na ambata a baya yan tagwayen nan 23 (da idan sun hade na mace da na namiji ke samar da kwayoyin chromosomes 46 na sabuwar halitta) to a tagwayen na 23 na mace, zaka samu duk biyun dogwaye ne amma a na namiji guda daya dogo ne dayan kuma gajere. To a wajen garwaya su, idan dogo na mace ya hadu da dogo na namiji (wato su ka zama duk dogwaye ke nan) sai abinda za’a haifa ya zama namiji. Idan kuma na mace dogo ya hadu da na namiji gajere (wato dogo da gajere su ka hade) sai jaririyar ta zama mace. Kafin kimiyya ta habaka, ana tsammanin cewa gado a cikin jini ya ke tun zamanin su Aristotle shekaru 2500 da su ka gabata. Amma yanzu an gane cewa jini aikinsa daban. Akwai kwayoyin halitta na jini (Blood cells) kala uku, wato jajaye (red blood cell) wadanda ke baiwa jinin launinsa. Su ne ke dakon abinci, iska, da gubar da ake fitarwa daga jiki. Sai farare (White blood cell) wadanda aikinsu shine yakar kwayoyin cututtuka da kuma na karshen da ake kira platelets wadanda aikinsu shine daskarar da jini idan an ji ciwo kada jinin jiki ya tsiyaye. Bayanin karshe shine cikin suratul Hajj da Allah ke cewa; Q22:5 “”Lallai ne mu, mun halitta ku daga turbaya, sannan kuma daga gudan jinni, sannan kuma daga tsoka wadda ake halittawa da wadda ba’a halittawa.”

Me Allah ke nunawa anan da cewa tsoka da ake halittawa da wadda ba’a halittawa? Wato da farko ya dauko asalin samuwar halitta daga turbaya ko mu ce sinadarai wadanda da su aka gina jikunanmu. Sannan daga gudan jini da tsoka wanda bayani ya gabata. Sai kuma tsokar da ake halittawa da wadda ba’a halittawa. Wannan na bayani ne yadda surar dan tayi ke caccanzawa tun daga garwayayyen maniyi da kwan mace wanda a farko ke kamanni da talibanban, wato yayan kwadi. Sannan tsagun numfashi (Gill arches) irin na kifi su bayyana. Tsokokin a jejjera su kamar na dabbobin da can masu kashin baya kafin a juya su zuwa kwanji irin na dan Adam. Sannan jela ke fitowa a daidai kugu irin ta birai amma kafin haihuwa sai ta zuke ta koma. Duk wadannan siffofi na kwado, kifi, dabbobi masu kashin baya da biri ai kun ga a karshen halittar jariri duk bacewa su ke yi, shi ne abinda Allah ke nufi da wadanda ba’a halittawa. Amma Allah ya kawo su domin warwarar tarihin halittarmu a wannan duniya yadda muka biyo kafin zama mutum. Sai kuma a karshen karshe na wanna tsari Allah ya rufe da cewa; Q23:14 “Sannan muka halitta shi gudan jini, sannan mu ka halitta gudan jinin tsoka, sannan muka halitta tsokar ta zama kasusuwa, sannan mu ka tufatar da kasusuwan da wani nama (fata), SANNAN MUKA KAGA SHI, WATA HALITTA TA DABAN.”

Wato halitta da ta faro daga digon maniyya kwaya daya, ta bi matakai daban daban yadda kafin a sami cikakkiyar sura ta mutum idan aka fito maka da dan tayi aka ce mutum ne ba za ka yarda ba, wanda ke jaddada tarihinmu a baya (evolutionary past). A karshe duk a ka yi watsi da wadannan siffofi, aka kagi wata sura ta daban, wato ta mutum wadda ita ce ake haihowa kunshe da tiriliyoyin kwayoyin halitta. Wato Dan Adam dandazo ne na tiriliyoyin kwayoyin halitta, kuma ya faro ne daga kwayar halitta guda tamkar yadda halitta mai rai ta faro ta watsu ta fantsama. Tsarki ya tabbata ga ubangijin halitta gwani, masani.

Mu hadu a kashi na biyu domin dorawa daga inda mu ka tsaya.

4. Tsaunuka a matsayin turaka- Sun kawo maganar cewa a kimiyance kuskure ne da Qurani ya ce tsaunuka a doron Duniya na a matsayin turaku ne wadanda ke rike kasa. Sun kawo ayar; Q78:7 “Da duwatsu turaku (ga rike kasa).”

Domin a ganinsu, farantai na karkashin kasa da ke dauke da nahiyoyi (plate tectonics) su ne ke wannan aiki ba tsaunuka ba. Ba ya ga wannan aya sai Allah ya sake jaddawa a cikin; Q21:31“Kuma Mun sanya tabbatattun duwãtsu a cikin ƙasa dõmin kada ta karkata da su.”

Shin menene gaskiyar maganar? Duwatsu turaka ne da ke aiki domin rike kasa? A ayar sai Allah ya ce “tabbatattun duwatsu” wato abin nufi, ba daidaikun duwatsu a nan da can ba, a’a, wato jerin carbin duwatsu (mountain ranges) Allah ke magana, wadanda kusan kowacce nahiya akwai su wadanda asalinsu sun faro ne a wani lokaci. Wane lokaci ne wannan? Q88:17 & 20 “Shin ba za su yi duba ba… Zuwa ga kasa (doron Duniya) da yadda a ka shimfida (baza) ta?”

Shekaru 1200 da wannan kiran, amma sai a shekarar 1800 Alexander Von Humboldt ya fara nazarin doron kasa ya kuma fara tunanin cewa ko dai nahiyoyin duniya da ke kewaye da tekun Atlantika a shekarun baya a hade su ke? Wannan tunani nasa bai yi tasiri ba sai bayan shekaru kusan sittin, wato a shekarar 1858 lokacin da shi kuma Antonio Snider ya kawo shawarar barbazuwar nahihoyi daga wata dunkulalliya guda daya (Pangaea ) abinda a kimiyya ake kira da “Continental drift” bayan ya yi nazarin gabobin tekun Atlantika a Afirka da kudancin Amurka wadanda kamar bakin almakashi za su iya hadewa da juna. Bayan nazarin yanayin kasar wuraren da kasusuwan halittun dabbobi da su ka shude da ke kamanceceniya da juna a gabobin guda biyu, ya nuna cewa hakika a shekarun baya wadannan gabobin a hade su ke.

A shekarar 1912 kuma, sai Alfred Wegener ya bijiro da kwararan hujjoji na bincikensa da ya tabbatar da cewa hakika wadannan gabobin na tekun Atlantika a baya sun kasance a hade har da nahiyar Turai, kafin su balle, kuma nahiyar Amurka ta yi yamma. Sannan ya kuma nuna cewa akwai irin wannan dangantaka tsakanin nahiyoyin Afirka, Antaktika, Australiya da Indiya miliyoyin shekaru da su ka gabata.

Ana kyautata zaton cewa nahiyar Amurka ta kudu da Afirka sun balle daga juna a karshen zamanin cretaceous, wato kimanin shekaru miliyan 100 da su ka wuce. Haka nan ita ma nahiyar Turai a wannan lokaci ta balle daga Amurka ta kudu, abinda ya haifar da shi kansa tekun Atlantika. Tekun Indiya kuma ya fara budewa ne tun a zamanin Jurassic, wato shekaru miliyan 150. Amma dai mafi girman ballewar a karshen zamanin cretaceous din ne suka faru, lokacin da zirin Indiya ya balle ya yi arewa har sai da ya ci karo da nahiyar Asiya. Ita kuma nahiyar Australia ta balle daga nahiyar Antaktika. To bayan wannan ballewar nahihoyi daga dunkulalliyar kasa guda daya (Pangaea) shi ne Allah ya ce bamu lura ba yadda aka baza kasa? To menene sakamakon wannan barbaza nahiyoyi? Q21:31 “Kuma Mun sanya tabbatattun duwãtsu a cikin ƙasa dõmin kada ta karkata da su.”

Wato ballewar Amurka ta kudu da ta yi yamma, shine abinda ya haifar da jerin carbin da ake kira da Cordirellan mountains, wato duwatsun da ke yammacin nahiyoyin Amurka ta Arewa (Canada da Amurka) wato duwatsun Sierra Nevada da Rocky mountains. Da kuma na Amurka ta kudu, wato jerin carbin duwatsun Andes.

Haka nan zirin Indiya da ya doshi Arewa inda ya ci zango mai nisa kafin cin karo da Asiya, shi kuma ya haifar da jerin carbin Himalayas. Jerin carbin duwatsun Alps da ke Turai da na Atlas da ke Afirka kuma sun samu ne sakamakon matsewar kudu da Arewa na nahiyoyin guda biyu. Don haka jerin carbin wadannan nahiyoyi sun taimaka waje baiwa nahiyoyi daidaito sun zauna daram a kan farantai (tectonic plates) da ke dauke da kowacce nahiya bayan wannan ɓallewa.

Ba a nan abin ya tsaya ba, domin a karkashin Teku ma akwai jerin carbin duwatsu wadanda suke samuwa sakamakon motsin farantai da ke dauke da nahiyoyi. Idan wadannan farantai su ka motsa baya da juna, shi ke haifar da jerin carbi duwatsu masu aman wuta a Teku (mid-ocean ridge) idan kuma a karkashin kasa ne, sai ya haifar da kwazazzabo, kamar babban kwazazzabon (Great Rift Valley) da ya taso tun daga Syria har zuwa Mozambique a Afirka.

A kuma inda wadannan farantai ba ja baya su ka yi da juna ba, misali idan karo su ka yi, daya daga cikin farantan sai ya haye saman dayan abinda ke haifar da wasu jerin carbin duwatsu masu aman wuta (volcanic) da ake kira Arc. Duk lokacin da wadannan farantai su ka ci karo da juna ya kan haifar da jerin carbin duwatsu. Wadannan jerin carbin duwatsu kuma su ne ke baiwa nahiyoyi daidaito babu tangal-tangal, abinda ayar ta jaddada; Q21:31 “Kuma Mun sanya tabbatattun duwãtsu a cikin ƙasa dõmin kada ta karkata da su.”

Shin Qurani ya yi kuskure wajen cewa duwatsu turaku ne ga kasa?

5. Duniyoyi- Wato adadin duniyarmu a cikin suratul Dalak da Allah ya ce; Q65:12 “Allah, wanda Ya halitta bakwai ɗin sammai kuma da ƙasã kwatankwacinsu.”

Wato ba ma masu kalubalantar Qurani ba, hatta akasarin musulmi na daukar cewa wannan aya na nufin cewa akwai Duniyoyi bakwai kamar sammai. Abu na farko da zamu fara fahimta shine, Duniyoyi a iya ilimin da Dan Adam ya ke da shi a yau, sun kai a kiyasce kimanin tiriliyoyi. Don haka Allah da ya halicce su ne kuma zai ce kasa irinta bakwai ce kacal? Ko alama. Kalmar “Misluhunna” wato kamanni, ko mu ce kamanceceniya da Allah ke magana akan sammai bakwai da kasa, ba na adadi ba ne, na yanayi ne. Saboda da sammai da Duniya dukkansu sun faro ne daga asali guda, kamar yadda Allah ya fada a suratul Anbiya Q21:30. Kuma sammai ta faro daga sinadarai (elements) na Hydrogen da Helium (Uba Da Uwa ke nan nan duk wani sinadarin halitta mara Rai, wato matter). Wannan auratayya ita ta haifar da sauran sinadarai (Chemical elements da ke periodic table) wadanda su ka yi sammai da duk abinda ke cikinta. Ba a gane wannan ba tsawon karnoni 12 har lokacin da masanin kimiyya Joseph Fraunhofer ya gano bangaren ilimin spectroscopy inda Fraunhofer ya fitar da layukansa wadanda ke bada damar gane sinadarin da ke cikin halittun sammai ta hanyar launinsu.

To, an sami lokatai uku na haihuwar sinadarai a sammai tun bayan samuwar sammai daga Big Bang, wadda ta fara daga Hydrogen da Helium da suka samar da akasarin taurari. Sannan sai Yayansu, da aka samar a cikin taurari (stellar nucleosynthesis) wato sinadarai irin su carbon, nitrogen da oxygen wadanda su ka samar da halittu irinmu. Sai kuma jikokin sinadaran wadanda su ke samuwa yayin mutuwar taurari a lokacin da su ke yin bindiga su ka tarwatse, a wannan lokaci ake samar da sinadarai masu nauyi irinsu karfe (iron), gwal (gold) da nickel.

To kun ga a takaice Allah na gaya mana cewa, Duniya na kamanceceniya da sammai, ba ta adadi guda bakwai ba ne, ta yanayin sinadarai ne da suke ginin bulon duk wata halitta a cikin sammai da kasa.

Bari mu dakata a nan… Za mu ɗora daga inda mu ka tsaya insha Allah a maƙala ta gaba.

Malam Ali Abubakar Sadiq manazarci ne a Jihar Kano. Za a iya tuntuɓar sa a lambar wayarsa 08039702951

By ukarofi