Zargin ɓatanci: Kotu ta ayyana 19 ga Yuni a matsayin ranar gurfanar da Natasha

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta ayyana 19 ga watan Yuni, 2025 a matsayin ranar da za a gurfanar da dakatacciyar Sanata, wato Natasha Akpoti-Uduaghan a gabanta.

An maka ta ne a gaban kotun bisa tuhumar ta da laifin ɓata suna ga wasu sanannun jagororin siyasa.

Gwamnatin Tarayya ta shigar da ita ƙara ne a kotun bisa zargin ta da furta kalaman ɓatanci akan shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da kuma tsohon gwmanam jihar Kogi, Yahaya Bello.

Da fari dai an zaɓi ranar 3 ga watan ne, inda daga bisani aka sauya lokacin saboda jinkiri da aka samu wajen shirya takardun da ke ɗauke da batun.

Natasha ta yi ikirarin cewa, gaskiyar al’amarin zai bayyana a yayin aka tsaya a gaban kotu.

By Babaji