Ƙungiyar Editocin Nijeriya na shirin zaɓar sabbin jagorori yayin taronsu a Enugu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar Manyan ƴan Jaridu ta Ƙasa, wato Nigerian Guild of Editors (NGE) za ta gudanar da babban taron mambobinta na Biennial National Convention a Enugu, daga ranar 26 zuwa 29 ga watan Yuni, 2025 mai taken ‘Building a Secure and Cohesive Nigeria: The Role of Dailogue, Inclusion, and the Media’.

A sanarwar da Shugaban ƙungiyar, Mista Eze Anaba da Sakatarenta, Iyobosa Uwugiaren suka fitar, NGE ta ce taron zai hada aƙalla sama da editoci guda 400 da wasu sanannun mutane.

Ministan Labarai da Wayar da Kai, Ahaji Mohammed Idris shi ne wanda zai jagoranci buɗe taron a yayin da Gwamnan Enugu, Peter Mbah shi ne mai masaukin baƙi.

Sannan, akwai Darakta Janar na rundunar ƴan sandan farin kaya a jihar, Mista Adeola Oluwaseun wanda zai gabatar da jawabi game da hasashen al’amarin tsaro a ƙasar.

Haka kuma NGE ta ce tana koƙarin tabbatar da an sauke nauyin aikin jarida wajen wayar da kan al’umma akan muhimmanci tsaro a ƙasa da tabbatuwar ci-gaba.

By Babaji