Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau
Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Bungudu da Maru a Jihar Zamfara Hon. Abdulmalik Zubairu a ranar Lahadi ya saki kuɗi Naira miliyan 97 don biyan kashi na biyu na shirin bayar da tallafin karatu ga ɗaliban manyan makarantun gaba da sakandare a faɗin Najeriya a mazaɓar sa.
Wannan ƙari ne akan Naira Miliyan 120 da ɗan majalisar ya biya tun farko a matakin farko na tallafin karatu ga ɗalibai a mazaɓar sa ta Bungudu da Maru a 2025.
A jawabin sa Hon. Zannan Bungudu wanda Shugaban Kwamitin tantance ɗaliban ya wakilta, Hon. Bashir Bello Auki yace an tsara shirin ne ga duk ɗalibai na mazaɓar ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa ba.
“Idan aka zo batun ilimi musamman wannan batu na bayar da tallafin karatu, kowane mazaɓa na da damar cin gajiyar ba tare da la’akari da siyasa ba” Zannan Bungudu ya bayyana.
Shima da yake jawabi, shugaban kwamitin bayar da tallafin karatu da ilimi Muhammad Lawal Adamu ya bayyana cewa kwamitin bayar da tallafin zai yi duk mai yiwuwa don ganin an gudanar da aikin ba tare da tangarɗa ba.
A cewarsa, tuni kwamitin ya rubutawa makarantu da magatakardu na dukkan manyan makarantun Najeriya suna neman bayanan duk ɗaliban ƙaramar hukumar Bungudu da Maru da suka yi rajista a irin waɗannan makarantun.
Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa a wannan kashi na biyu shiyyar Kaduna tana da dalibai 614, Sokoto zone 622, COE Maru 755 da Abdu Gusau Polytechnic Talata Mafara tana da ɗalibai 558.
Hakazalika Aminu Lawal Bungudu mai magana da yawun Hon. Abdulmalik Zubairu ya bayyana cewa ana biyan ɗaliban jami’a Naira 40,000 kowannen su, yayin da ɗaliban Polytechnic da Monotechnic ana basu Naira 30,000 kowannensu.
