Yanzu-yanzu: Sufeton ƴan sanda ya je Benuwai, ya baza jami’ai domin daƙile kashe-kashe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sufeton ƴan sanda (IGP), Kayode Egbetokun ya je Jihar Benuwai dake Arewa ta Tsakiya, inda wasu mahara suka farmaki al’umma a ranar Juma’a da kashe da dama daga cikinsu tare da ɗaiɗaita wasu ɗaruruwa.

Jihar Benuwai tana fama da matsalolin kashe-kashe na tsawon shekaru a sakamakon faɗar ƙabilanci da ke tsakanin manoma da makiyaya.

Saidai, a ƴan kwanakin nan wasu mahara ne ke ƙaddamar da hare-hare a ƙauyukan dake sassan jihar.

Kimanin mutane 160 ne aka kashe a makonni kaďan da suka gabata, lamarin da ya jefa al’ummar jihar halin zaman ɗar-ɗar.

A ranar Lahadi ne Shugaba Bola Tinubu ya umarci jagororin tsaro da su gaggauta aiwatar da umarnin da ya musu a baya na su samar da zaman laifin da tsaro a jihar.

By Babaji