Daga USMAN KAROFI
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ɗage ziyararsa da aka shirya a Jihar Kaduna domin ya mayar da hankali kan rikicin da ke addabar Jihar Benuwai.
A ranar Laraba, 18 ga Yuni, 2025, Shugaba Tinubu zai kai ziyara Jihar Benuwai domin duba halin da ake ciki da kuma lalubo hanyoyin wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’ummomin da rikicin ya shafa.
A cikin wannan ziyara, ana sa ran shugaban zai gana da shugabannin gargajiya, na addini, na siyasa da kuma matasa domin tattaunawa kan hanyoyin da za a bi domin kawo ƙarshen tashin hankalin.
Tun kafin zuwansa, Shugaba Tinubu ya tura wasu manyan jami’an gwamnati ciki har da sakataren gwamnati, sufeton ƴan sanda, Shugabannin harkokin tsaro da kuma Shugabannin Kwamitocin tsaro na Majalisa zuwa jihar domin shiryawa taron.
A cewar mai ba shugaban shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, shugaba Tinubu ya bayyana alhininsa kan hare-haren da suka ci gaba da faruwa a Benuwai, inda ya buƙaci al’umma su rungumi zaman lafiya da juna. Ziyarar da aka shirya a Kaduna za a ɗaga zuwa Alhamis, 19 ga Yuni, domin bai wa ziyarar Benuwqi mahimmanci.
