Obasanjo zai ƙaddamar da ayyuka a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Tsohon shugaban ƙasar tarayyar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo na shirin kai ziyara Jihar Zamfara domin ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnan Jihar Zamfara mai ci Dauda Lawal ya aiwatar a cikin shekaru biyu da yayi yana mulki.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasar zai ƙaddamar da asibitin ƙwararru na Yeriman Bakura wanda gwamnatin Dauda Lawal ta gyara gaba ɗaya wanda aka tanadar da kayan aiki na zamani.

Bugu da ƙari, tsohon shugaban ƙasa Obasanjo zai ƙaddamar da manyan tituna a yankin GRA Gusau, waɗanda ke cikin aikin sabunta biranen gwamnatin.

Sanarwar ta ce, tsohon shugaban ƙasa Obasanjo zai isa Gusau ranar Talata 17 ga watan Yuni domin ƙaddamar da ayyukan.

By ukarofi