Kotu ta yi watsi da buƙatar Gwamnatin Tarayya ta kama Natasha kan zargin ɓatanci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Litinin ne Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar Gwamnatin Tarayya ta neman a bada izinin kama Sanatar Kogi Ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan.

Hakana ya biyo bayan rashin zuwa kotu da ta yi kan zargin ɓatanci da ta yi akan wasu manyan ƴan siyasa.

Mai Shari’a Muhammed Umar a yayin sauraron ƙarar, ya ce ba a gabatar wa Natasha saƙon tuhumar ba a hukumance, don haka ba lallai ba ne sai ta gurfana a kotun ba.

Saboda haka ne alƙalin ya ce ba za a amince da buƙatar gwamnatin ba kasancewar babu hujjar mai ƙarfi da ke tabbatar da rashin biyayyar sanatar.

Da ya ke jawabi, lauyan da ke kare ɓangaren gwamnati, David Kaswe ya ce tunda an bai wa lauyan Natasha saƙon tuhumar, hakan ya nuna cewa ta san abinda aka shigar da ita ƙara a kai wanda ya wadatar da su biyun.

Daga nan ne kotun ta yanke hukuncin sake zama akan batun zuwa ranar 30 ga watan Yuni, 2025 domin gurfanar da ita a gaban kotu.

By Babaji