Gwamnatin Katsina ta jaddada matsayinta na ba za ta yi sulhu da ‘yan ta’adda ba

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro a Jihar Katsina Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya shaidawa manema labarai haka a ofishin sa.

Ya ce gwamna Dikko Raɗɗa ya riga ya faɗa ya nanata matsayin sa na ba zai sasanci da ‘yan ta’adda ba .

Sai dai kwamishinan ya bayyana cewa sakamakon addu’a da al’ummomi ke yi wasu shugabannin yan ta’addan a ƙananan hukumomin Jibiya, Batsari, Ɗanmusa da Safana suka buƙaci zaman sasanci da al’ummar yankunan.

“Sun zauna da shugabannin al’ummar ƙananan hukumomin inda su kayi yarjejeniya dukkan su ɓangaren biyu suka sanya wa hannu”inji kwamishinan.

Dr Ɗanmusa, ya ƙara da cewa waɗannan ‘yan ta’addan sun miƙa wasu da cikin makaman su tare da sako waɗanda sukai garkuwa dasu.

Dr Nasiru Ɗanmusa ya bayyana cewar gwamnatin Jihar da haɗin gwiwar jami’an tsaro za su cigaba da yaƙar ‘yan ta’adda a ƙananan hukumomi irin su ƙanƙara, Faskari Ɗandume, Sabuwa da ba ayi zaman sulhu da suba.

Watanni huɗu kenan da zaman sasanci a ƙananan hukumomin Batsari da Jibiya ba a samu wani rahoton ta’addan ci ba a yankunan.

Haka ma a ƙananan hukumomin Ɗanmusa da Safana da akai zaman sasanci kusan mako guda da ya wuce babu wani rahoto na kai hare hare a yankunan.

Kwamishinan tsaro Dr Ɗanmusa yayi gargaɗi ga ‘yan ta’adda na ƙananan hukumomin da akai sasanci cewa duk wanda aka samu da saɓa yarjejeniya da akayi za a ɗauki mataki a kan sa.

Harkokin kasuwanci da zirga zirga na ababe na hawa ya dawo gadan gadan a waɗannan yankuna.

By ukarofi