Daga USMAN KAROFI
Ma’aikatan hukumar kula da ’yan gudun hijira (NCFRMI) sun kulle ofishin babban birnin tarayya Abuja a wani gangamin nuna rashin amincewarsu da shugaban hukumar, Aliyu Ahmed. Sun buƙaci a gaggauta sauke shi daga muƙaminsa, suna zargin sa da cin hanci, rashin kulawa da walwalar ma’aikata, da kuma karkatar da kuɗaɗen hukumar, musamman na asusun kula da muhalli.
Wani babban jami’in hukumar da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce duk da aika takardu da dama dangane da raba kayan agaji ga ‘yan gudun hijira, jihar Nasarawa kawai ke ci gaba da amfana yayin da sauran ofisoshin jihohi ke tashi babu komai. Haka kuma, akwai jinkirin biyan kuɗin tafiya ga ma’aikata duk da cewa an riga an saki kuɗaɗen.
Ma’aikatan sun bayyana cewa har yanzu an kasa bayyana gaskiyar yadda aka rarraba motocin da aka bayar da gudunmawa don aiki a ofisoshin jihohi. Ma’aikatan sun yi kira da a aiwatar da sauye sauye cikin gaggawa, musamman a fannin jin daɗin ma’aikata da gaskiya wajen tafiyar da kuɗaɗe, tare da ɗaukar matakin sauya shugabanci.
