Abinda ya sa na tsame sunan Shettima yayin ambatar Tinubu – Mataimakin Shugaban APC a Arewa ta Gabas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin Shugaban APC na Ƙasa a Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu, ya bayyana dalilansa na ƙaddamar da Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar da zai wakilci jam’iyyar a babban zaɓen 2027 ba tare da haɗa shi Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ba, lamarin da ya nuna cewa akwai ƙamshim gaskiya a jita-jitar rikicin cikin gida a APC.

Salihu, a yayin hira da gidan talabijin na Channels, ya ce rashin ambatar Tinubu tare da Shettima a taron jam’iyyar na Shiyyar Arewa maso Gabas da aka yi a Jihar Gombe ya yi daidai da tsarin babban taron jam’iyyar da kuma dokokinta.

Ya ce, a cikakken jawabinsa ya yabi Shettima a inda ya bayyana shi a matsayin ɗan yankin Arewa maso Gabas kuma wanda mutanen shiyyar suke goyon bayansa tare da alfahari da shi.

Haka kuma, ya ce a taron ne ya yaba wa Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribaɗu bisa ƙoƙarinsa da sauran masu riƙe da manyan muƙaman Gwamnatin Tarayya ƴan Shiyyar kafin ya ayyana Tinubu a matsayin ɗan takara ɗaya tilo daga APC.

Sannan, ya ƙara da cewa a yayin taron zaɓen fidda gwani, ana ayyana sunan mai nema zama shugaban ƙasa ne kaɗai ba da abokin tafiyarsa ba.

A dalilin haka ne Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe da takwaransa na Gombe, Inuwa Yahaya suka yi irin haka wajen ayyana Tinubu kaɗai duk da cewa sun yaba wa Shettima a gefe guda.

A lokacin da ya ke tsokaci game da raďe-raďen ko akwai rikici tsakanin Tinubu da Shettima, Muhammad Salihu ya ce ba gaskiya bane zancen, yana mai bayyana hakan a matsayin abinda aka ƙirƙira domin ruɗar da al’umma daga masu ƙoƙarin haddasa rikici a tsakaninsu.

By Babaji