Gwamna Raɗɗa ya ziyarci ɗaliban Katsina da ke karatu a Chana

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan ya kai wannan ziyara ce a jami’ar Xuzhou University of Technology da ke Jiangsu, China.

Ziyarar ta biyo bayan taron da gwamnan ya halarta a Macao, inda ya gana da mutane masu son zuba jari a Jihar Katsina.

Gwamna Raɗɗa ya kuma bayyana cewa, “nasararku nasararmu ce, za mu taimaka muku har ku gama Karatu cikin nasara.”

Ya kuma shawarce su da su riƙe addininsu da kyau, su zama jakadu nagari ga jihar su dama ƙasar baki ɗaya.

Ɗaliban sunyi godiya ga gwamnatin Dikko Raɗɗa, a inda suka ce za su yi amfani da damar da aka basu domin taimaka ma Jihar Katsina.

A cikin tawagar gwamnan akwai, mai ɗakinshi Hajiya Fatima Dikko Umaru Raɗɗa da kuma sakataren shi na musamman Abdullahi Aliyu Turaji da kuma Shugaban hukumar ruwa ta jiha, Dr. Tukur Tingilin da mai bashi shawara kan ci gaban al’umma Alhaji Haroun Abba Gana.

By ukarofi