
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi kira ga hukumomin EFCC DSS da NPF da su gudanar da binciken gano waɗanda ake zargi haɗa hannu da su wajen ba wa Adeyemi Adeniyi Matthew damar aiki da hukumar bogi ta “Presidential Foreign Intervention Promotion Council” (PCFIPC).
Rahotanni sun bayyana cewa, fadar a wata sanarwa da Mai Taimaka wa Shugaban Ƙasa akan Harkokin Yaɗa Labarai, Temitope Ajayi ya wallafa a kafar X ranar Asabar, ta ce wajibi ne a gano waɗanda suke da hannu a taimaka wa Adeniyi aiki da hukumar ƙasa ta bogi, a dakatar da kuma kama su don su fuskanci hukuncin da doka ta tanada.
A cewarsa, waɗanda ake zargin ba iya ba Adeniyi damar gudanar hukumar ba suke yi, har ma da yunƙurin neman a tsige shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.
Ya bayyana cewa, masu bincike a DSS, ‘yan sanda da EFCC suna da nauyin gano haƙiƙanin al’amarin da abin da ya sa aikin nasa ke gudana.
Haka kuma, mai taimaka wa shugaban ƙasar ya zargi Adeniyi da sauya akalar tunanin al’umma ta hanyar tsirar da zargin rashawa akan jami’an gwamnatin da nufin karkatar da hankali akan zarge-zargen badaƙalar da ke kansa.
