Faransa na karɓar baƙuncin taron tallafa wa Afrika don samar da rigakafin cutuka

Spread the love

A Alhamis ɗin nan ce, ake fara taron ƙasa da ƙasa a birnin Paris don tallafa wa Afrika wajen samar da alluran rigakafin cutuka, domin taimaka wa ƙasashen nahiyar cimma muradun samun kariya daga kamuwa da cutuka da kuma inganta lafiya nan da zuwa shekarar 2030.

An shirya gudanar da taron ne a ƙarƙarshin haɗin gwiwar gwamnatin Faransa da ƙungiyar ƙasashen Afirka AU, sai ƙwararru daga ƙasashen Turai, da kuma shirin Gaɓi da ke taimaka wa wadatar alluran rigakafi ga yara a ƙasashe marasa ƙarfi.

Muhimmin batun da taron zai mayar da hankali akai shi ne kafa gidauniyar maƙudan kuɗaɗen da za a yi amfani da su wajen ƙaddamar da shirin fara samar da alluran rigakafin cutuka a ƙasashen Afrika, sabon babin da ake fatan ya fara tasiri daga shekarar 2026 zuwa 2030, lokacin da ake sa ran an cimma muradun cigaban da aka sanya gaba.

A ranar Litinin ɗin da ta gabata, gwamnatin Faransa ta ce, ita kanta, da ƙungiyar Tarayyar Turai da Canada, da Italiya da Japan da Korea ta Kudu da kuma Amurka, sun yi alƙawarin bayar da tallafin fiye da dala biliyan guda domin samun nasarar shirin na Gaɓi, wanda zuwa ƙarshen shekarar bara ta 2023, ya sanar da samun nasarar yi wa ƙananan yara sama da biliyan ɗaya a sassan duniya alluran rigakafin cututuka daban daban.

By ukarofi