Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya yi tashin gwauron zabi da kusan kashi 5 cikin ɗari a ranar Litinin, sakamakon ƙara tsananta rikicin da ke tsakanin Isra’ila da Iran, lamarin da ya janyo fargabar samun tangarɗa wajen samar da mai a duniya.
Rahotanni sun nuna cewa farashin ɗanyen man Brent, wanda ake amfani da shi a matsayin ma’aunin kasuwannin duniya, ya kai dala 97.69 kan kowace ganga, wanda ya nuna ƙarin kusan kashi 4.9 cikin ɗari idan aka kwatanta da dala 93.09 da aka rufe kasuwa da ita a baya.
Haka kuma, farashin ɗanyen man West Teɗas Intermediate (WTI) na Amurka ya haura zuwa dala 94.49 kan kowace ganga, bayan ya tashi da kusan kashi 4.5 cikin ɗari daga dala 90.54 da aka yi ciniki da ita a zaman baya.
Tashin farashin ya biyo bayan sabbin hare-haren da ɓangarorin biyu suka kai wa juna, wanda ya ƙara tayar da hankalin masu zuba jari da masu ruwa da tsaki a harkar makamashi.
A ranar Litinin, wani harin sama da Isra’ila ta kai ya afkawa wani katafaren kamfanin sarrafa sinadarai na Karun Mahshahr Petrochemical Company da ke garin Mahshahr a kudu maso yammacin Iran.
Mataimakin gwamnan lardin Khuzestan mai kula da harkokin tsaro, Valiollah Hayati, ya bayyana cewa wasu makamai masu linzami sun bugi wani sashe na harabar masana’antar, lamarin da ya haddasa ɓarna a wasu gine-gine. Sai dai ya ce babu rahoton rasa rai a harin, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr ya ruwaito.
A gefe guda kuma, an ji karar ƙararrawar gaggawa a wasu sassan tsakiyar da kudancin Isra’ila bayan Iran ta harba makamai masu linzami zuwa cikin ƙasar.
A cewar rundunar sojin Isra’ila, tsarin kariyar sararin samaniyar ƙasar ya yi nasarar tarwatsa wasu daga cikin makaman kafin su kai ga inda aka nufa.
Rahotanni sun ce an ji ƙarar fashe-fashe a yankuna da dama ciki har da birnin Kudus (Jerusalem) da kuma yankin Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ke mamaye da shi, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin daƙile hare-haren.
Da daddare kafin hakan, Iran ta ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami da dama zuwa Isra’ila, lamarin da ya sa aka sanya yankunan arewacin ƙasar cikin shirin ko-ta-kwana.
Mahukuntan Isra’ila sun bayyana cewa an harba kusan makamai masu linzami goma, yayin da rundunar sojin ƙasar ta ce ta kai hare-haren ramuwar gayya kan wasu wurare a yammaci da tsakiyar Iran.
Har ila yau, Isra’ila ta ɗan dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a sararin samaniyarta bayan ta ce ta daƙile wani makami mai linzami da aka harba daga Yemen.
Tashar talabijin ta Channel 12 ta Isra’ila ta ruwaito cewa matakin ya biyo bayan ƙararrawar gaggawa da aka kunna a yankin Tel Aviv da wasu sassan tsakiyar da kudancin ƙasar.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce tsarin kariyar sararin samaniyarta ya yi nasarar kakkaɓo makamin kafin ya haddasa wata illa.
Masana harkar makamashi na ganin cewa idan rikicin ya ci gaba da ƙamari, akwai yiwuwar farashin mai ya ci gaba da tashi, musamman idan hare-haren suka shafi manyan cibiyoyin samar da mai da iskar gas a yankin Gabas ta Tsakiya.
