Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A wani mataki na samun daidaito a ɓangaren man fetur, ƙungiyar Manyan Dillalan Man Fetur na Nijeriya, MEMAN ta bayyana cewa farashin man fetur ya sauka zuwa N970 a watan Disamba 2024, daga N971 kowace lita.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da farashin ɗanyen mai ya yi ƙasa da dala 73.77 a ranar Laraba, daga dala 74 a makon jiya.
Sai dai a cikin sanarwar ta rahoton makamashin yau da kullum da Blueprint Manhaja ta samu, ta bayyana cewa sabon farashin ya dogara ne akan Naira 1,533.57/$ da dala 73.91 kan kowacce ganga ta ɗanyen mai.
Duk da haka, ya kuma bayyana cewa: “Farashin albarkatun man fetur na ƙasa da ƙasa yana fuskantar gagarumin sauyi saboda yanayin siyasa da tattalin arziki, ciki har da abubuwan da suka faru a Gabas ta Tsakiya, yanayin kasuwannin ƙasar Sin, da kuma sakamakon zaɓen Amurka na baya-bayan nan.
“Haka zalika farashin canji na ƙasashen waje yana fuskantar sauyin yanayi. Farashin sauka, kasancewar waɗannan abubuwan suna tasiri sosai, yana iya canzawa sau da yawa a rana tsaka.”
Sai dai har yanzu farashin man fetur bai canza ba kan Naira 1,025 ga kowace lita a Legas.
Shugaban ƙungiyar reshen jihar Legas, Ehimen Joseph, ya ce: “’Yan kasuwa ne ke ƙayyade farashin man fetur a ƙarƙashin tsarin kasuwancin da aka yi. Faɗuwar farashin mai yiwuwa ne.”
Hakazalika, babban jami’in cibiyar bunƙasa sana’o’in hannu (CPPE), Dakta Muda Yusuf, shi ma ya ce, “Farashin man fetur ba zai iya faɗuwa haka kawai ba, domin ‘yan kasuwa na da jari mai yawa. Har sai an gama, ba za su rage ba.
“Amma faɗuwar farashin yana yiwuwa a kan lokaci bisa ƙarfin kasuwa da canjin kuɗaɗen waje. A wasu kalmomi, rage farashin man fetur ba zai iya zama kwatsam ba. Kasuwar ba shakka za ta samu koma baya, wanda zai ɗore a cikin wata ɗaya ko biyu da ke jiran taɓarɓarewar hannun jarin da ‘yan kasuwar suka yi da kuma canjin kuɗaɗen waje mai ɗorewa.”
