Farfaɗo da DMCSA ya samar da wadatattun magunguna a asibitin Sir Muhammadu Sunusi – Pharm. Nafisa Bashir

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugabar Sashen Magunguna na Asibitin Kwararru na Sir Muhammadu Sunusi, Pharm. Nafisa Muha Bashir, ta ce farfaɗo da Hukumar Drug Management and Commodity Supply Agency (DMCSA) da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi ya taimaka wajen samar da wadatattun magunguna masu inganci da araha a asibitin.

Ta bayyana cewa yanzu marasa lafiya na samun magunguna da farashinsu ya ragu da fiye da kashi 60 cikin 100 idan aka kwatanta da farashin kasuwa, tare da tabbatar da ingancin magungunan.

A cewarta, wasu magunguna ana ba da su kyauta musamman ga mata masu juna biyu, lamarin da ta ce ya nuna ƙudirin gwamnatin jihar wajen inganta harkokin lafiya.

Pharm. Nafisa ta yabawa Babban Daraktan Asibitin, Dr. Usman Tijjani Aliyu, bisa jajircewarsa wajen tabbatar da ingantaccen kula da marasa lafiya.

Ta ce shugabancinsa ya sa ma’aikatan asibitin ke gudanar da aikinsu da ƙwazo, domin yana yawan zagayawa sassa daban-daban na asibitin tare da duba yadda ake kula da marasa lafiya.

Ta ƙara da cewa irin wannan tsarin shugabanci ya ƙara wa jama’a kwarin gwiwar neman magani a Asibitin Kwararru na Sir Muhammadu Sunusi da ke Kano.

By ukarofi

Leave a Reply