Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau
Sabon shugaban jami’ar tarayya da ke Gusau FUGUS, Farfesa Tukur Adamu ya kama aiki.
Farfesa Tukur Adamu shi ne shugaban jami’ar na huɗu da ya karɓi ragamar mulki daga shugaban jami’ar mai barin gado Farfesa Mu’az Abubakar Gusau.
Farfesa Mu’az Abubakar Gusau ya jagoranci Jami’ar daga 2021 zuwa 2026 a matsayin shugaban jami’a na uku.
Da yake jawabi a lokacin miƙa mulkin, shugaban jami’a mai barin gado Farfesa Mu’az Abubakar Gusau ya gode wa shugabanin gudanarwar jami’ar, masu ruwa da tsaki da kuma al’ummar Jami’ar bisa goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake riƙe da muƙamin shugaban jami’ar.
Farfesa Mu’az ya yi kira ga sabon shugaban jami’ar da ya ci gaba da haɓaka Jami’ar a fannin koyarwa, bincike da tsarin ilmantarwa.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan amsar ragamar Jami’ar, sabon shugaban jami’a Farfesa Tukur Adamu ya yi alƙawarin yin aiki tare da shugabanni, al’umma da kuma duk masu ruwa da tsaki don haɓaka jami’ar.
“Zan yi duk abin da ya dace don tabbatar da haɗin kai tare da kowa a Jami’ar don haɓaka jami’ar”. Ya ce
Farfesa Adamu ya yi kira ga shugabannin jami’ar, masu ruwa da tsaki da kuma al’ummar Jami’ar da su ba shi duk wani goyon baya da ake buƙata don kawo cigaba mai ma’ana a jami’ar.
