Fasinjoji sun shiga ƙunci a titin Maiduguri zuwa Damaturu bayan Boko Haram ta farmaki sansanin sojoji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗaruruwan matafiya ne suka shiga mawuyacin hali a safiyar yau Juma’a a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu bayan wani farmaki na cikin dare da mayaƙan Boko Haram suka kai wa wani sansanin sojoji a kusa da garin Ngamdu da ke da nisan kasa ƙasa da kilomita 50 daga Damaturu, Babban Birnin Jihar Yobe.

Lamarin da ya tilasta wa sojoji rufe titin, wanda al’umma ke yawaita zirga-zirga akansa domin harkokin kasuwanci da wasunsu a yankin na Arewa maso Gabas.

Shaidu da masu ababen hawa sun shaida wa manema labarai cewa, a harin ne aka yi ba-takashi da tayar da boma-bomai a kewayen Ngamdu tsakanin ɓangarorin biyu, lamarin da ya sa sojojin suka rufe babbar hanyar daga kowane ɓangare don kauce wa rutsawa da fararen hula da farmakin da ka iya shafar su.

Wani shaida ya ce, tun da safiyar Juma’ar ne sojojin suka rufe titin wanda hakan ya sa ɗaruruwan motoci suka jeru yayin da suke jira a buɗe domin su cigaba da zirga-zirgarsu.

Haka ma wani da aka yi hira da shi ta wayar salula ya ce, “babu wanda ake bari ya wuce. Har cikin dare mun yi ta jin ƙarar harbi.”

Wata mai suna Aisha Mohammed, wadda ta taso daga Maiduguri zuwa Potiskum ta ce mata da dama da yara ƙanana sun shiga ƙunci a yayin da aka rasa ruwa da abinci a motocinsu.

Majiyoyin sojoji sun tabbatar wa manema labarai faruwar al’amarin inda suka ce an nufi kai harin ne a sansanin sojoji da ke Ngamdu, wanda ɗaya ne daga cikin sansanonin soji da aka kafa da nufin katse zirga-zirgar mayaƙan tsakanin Borno da Yobe.

By Babaji