Filato: An kashe ɗan bindiga ɗaya a yunƙurin kai hari na uku a makarantar NIPSS

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI, Jos

Jami’an tsaro sun samu nasarar halaka wani ɗan bindiga ɗaya, cikin gungun wasu ýan bindiga da suka sake yunƙurin kai hari Cibiyar bada horo kan dabarun jagoranci ta ƙasa dake Kuru a kusa da Jos a karo na uku.

Lamarin ya faru ne cikin daren Laraba, yayin da maharan suka gamu da turjiya daga haɗin gwiwar jami’an tsaro na soja da ýan sanda da ke cikin shirin ko-ta-kwana, a dalilin haka aka samu nasarar kashe ɗaya daga cikin maharan, wasu kuma suka tsere da raunin harbin bindiga a jikinsu.

Mai magana da yawun cibiyar ta NIPSS, Osime Samuel, ya tabbatar da cewa, a wannan karon ma maharan ba su samu nasarar kutsawa cikin cibiyar ba, amma ana cigaba da bincike don gano su wane ne ke ƙulla waɗannan hare-hare da kuma manufarsu.

Idan ba a manta ba tun a ranar 16 ga watan Yuni na 2026 ake ta samun yunƙurin kai hari a wannan babbar cibiya ta ƙasa da ke horar da manyan jami’an gwamnati, har ma an kashe jami’an soja biyu da ɗan sanda guda ɗaya a harin farko. A dalilin haka aka sake girke ƙarin jami’an tsaro a cibiyar da kewayenta.

A wata ganawa da ya yi da manema labarai, babban daraktan cibiyar ta NIPSS, Farfesa Ayo Omotayo ya zargi ýan ƙabilar Berom dake ƙorafi kan kasancewar cibiyar a filin da suka ce gonakin kakaninsu ne aka karɓa ba tare da an biya diyya ba, da kuma Fulani makiyaya masu ɗauke da makamai da ke kiwo a kewayen cibiyar. Waɗanda ya ce dukkan su suna zama barazana ga zaman lafiyar mazauna cibiyar.

Sai dai ya ce, babu wata takamaimiyar hujja da ake da ita dake nuna cewa ga waɗanda suke da alhakin waɗannan hare-hare, sai binciken ýan sanda ne zai tabbatar da haka.

Wasu rubuce-rubuce da suke yawo a zaurukan sada zumunta na nuni da yadda ýan ƙabilar Berom suka ji zafin yadda babban daraktan na NIPSS ya danganta hare-haren dake faruwa a cibiyar kan ýan ƙabilarsu, suna masu cewa Berom mutane ne masu son zaman lafiya da karɓar baki. Wannan ta sa tilas babban daraktan ya fito ya nemi afuwar ýan ƙabilar Berom, yana mai cewa ba nufin sa ne ya ɓata musu suna ba.

Wannan dambarwa da ta taso ta buɗe wata zazzafar muhawara, inda wasu ke ganin bai kamata a cigaba da barin wannan cibiya a wajen ba, saboda tsaron rayukan mahalarta kwasa-kwasan da ake koyarwa, da kuma ma’aikatan cibiyar da iyalansu. Suna masu ba da shawarar ya kamata a mayar da wajen barikin sojoji, don inganta tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a yankin.

By ukarofi

Leave a Reply