FIRS ta gargaɗi Atiku kan siyasantar da tsarin haraji

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Tara Haraji ta ƙasa (FIRS) ta ƙaryata zarge-zargen da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi game da naɗa kamfanin ɗpress payments a matsayin ɗaya daga cikin manhajojin karɓar kuɗaɗen shiga. 

Hukumar ta ce, kalaman Atiku ba daidai ba ne, suna iya jefa tsarin kula da haraji cikin siyasa, alhali aikin na fasaha ne kawai ba na jam’iyya ba.

A ranar 19 ga Nuwamba, 2025 ne aka sanar da ɗpress payment solutions a hukumance a matsayin sabuwar hanyar karɓar kuɗaɗen shiga ta FIRS a tsarin ‘treasury single account’ (tsa). 

Sai dai a wata sanarwa da Atiku ya fitar daga baya, ya ce wannan mataki na da kama da tsarin “alpha beta” da ya taɓa aiki a Legas a zamanin Bola Tinubu, wanda ya yi iƙirarin cewa tsarin ya bai wa kamfani guda rinjaye haraji da kuɗaɗen gwamnati.

FIRS ta musanta hakan, inda ta ce babu kamfani guda da aka bai wa cikakken iko a tsarin. A cewar Arabinrin Aderonke Atoyebi, mataimakiyar shugaban FIRS kan yada labarai, tsarin da ake amfani da shi yanzu ya ƙunshi hanyoyi da dama na biyan haraji, ciki har da ƙuickteller, remita, etranzact, flutterwaɓe da ɗpresspay.

Ta ce, waɗannan PSSP ba su da ikon tarar kuɗi kai tsaye, kuma ba su karɓar kaso daga kuɗaɗen da ake biya. Ta ce duk kuɗaɗen da ake biya ta waɗannan tashoshi kai tsaye suke shiga asusun tarayya, ba tare da shiga hannun wani kamfani ba.

Atoyebi ta ƙara da cewa, gwamnati ta faɗaɗa hanyoyin biyan haraji ne domin a bai wa ‘yan kasa zaɓin amfani da dandalin da ya fi sauƙi gare su, tare da kawo ƙarin inganci, gaskiya da faɗakarwa ga al’umma. Ta ce wannan tsari zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, bunƙasa kasuwa da tabbatar da gaskiya a duk matakan karɓar haraji.

Ta kuma bayyana cewa ake gudanar da garambawul na kasa kan tsarin haraji ƙarƙashin kwamitin shugaban ƙasa kan manufofin kuɗi da haraji — wani babban tsari da ake amfani da shi domin inganta tattalin arzikin ƙasa. FIRS ta ce wannan gyara ba abin da ya kamata a jefa cikin taƙaddamar siyasa ba.

A ƙarshe, hukumar ta roƙi Atiku da sauran ‘yan siyasa su guji “maye ma’aikata da tsarin fasaha da siyasa”, domin haka kan kawo rudani ga jama’a. Ta ce tsarin haraji muhimmin ginshiƙi ne ga ƙasar, kuma bai kamata a karkatar da shi ba.

Irin waɗannan zarge-zarge suna iya jawo cikas ga nasarorin da ake samu a yaƙi da rashawa da inganta tattalin arziki, musamman idan jama’a suka fara kamewa wajen biyan haraji ko amfani da sabbin hanyoyi.

By ukarofi