Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Farashin kayan masarufi na cikin gida ya ci gaba da sauka a cikin shekara guda, abin da ya nuna tasirin raguwa a hauhawar farashi wadda ke saukowa a hankali a watannin baya-bayan nan.
Wannan ci gaba na faruwa ne yayin da farashin ɗanyen man fetur na brent crude ya koma Dala 62.09 a ƙarshen makon da ya gabata.
Bisa bayanan da Bismarck Rewane, shugaban kamfanin Financial Derivatives Company (fdc), ya fitar a rahoton kasuwanci na ƙarshen mako, farashin abinci da dama sun kai mafi ƙasa tun farkon shekarar nan. Ya ce shinkafa na kai N70,000, wake N65,000, yayin da garri ya tsaya a N20,000 — duk ƙasa da farashin su a wannan lokaci na shekarar 2024.
Rewane ya nuna cewa farashin kayan masarufi zai ci gaba da zama a dai-dai, sai ɗan ƙarin da ake sa ran ganin saboda bukatar kayan abinci da ke ƙaruwa a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.
Saukewar farashin abinci musamman ya taimaka wajen rage hauhawar farashi, wanda ya ragu tsawon watanni bakwai a jere. Masu nazari sun bayyana mamaki kan irin raguwar da aka samu a watan Oktoba.
A cewar afrinɓest, “rahoton cpi na watan oktoba 2025 ya nuna cewa hauhawar farashi ta sauka zuwa kaso 16.1 bisa ɗari daga kaso 18.0 bisa ɗari da aka samu a watan satumba.” Masu nazarin sun yi hasashen cewa zai tsaya a kaso 17.3 cikin ɗari, amma saukar ta fi tsammaninsu ƙarfi saboda tasirin binciken shekarar da ta gabata.
Sai dai rahoton ya nuna cewa a ɓangaren watan zuwa wata, hauhawar farashi ta ɗan tashi zuwa kashi 0.93 cikin ɗari, duk da cewa jimillar alamu na nuni da ingantuwar yanayin farashi a kasuwa.
Masu nazari sun ce saboda hauhawar farashi na nuni da matsakaita gangarar farashi gaba ɗaya, raguwar da ake gani a yanzu na nufin akwai ingantuwar yanayin ciniki da saukin farashin kayayyaki ga al’umma.
Amma a ɓangaren gwamnati, raguwar farashin ɗanyen man fetur na iya haifar da koma baya wajen samun kuɗaɗen shiga, musamman a lokacin da ake fama da ƙalubale wajen cike giɓin kasafin kuɗi.
A ƙarshen mako, farashin brent futures ya faɗi da kaso 2.07 cikin ɗari zuwa dala 62.09 bayan wani yunƙurin gwamnatin Amurka na matsa lamba wajen kawo sulhu tsakanin Rasha da Yukuren.
