Fitaccen ɗan wasan barkwanci, ‘Papa Ajasco’ ya kwanta dama

Daga WAKILINMU

Tsohon ɗan fim a masana’antar Nollywood, Femi Ogunrombi da aka fi sani da Papa Ajasco, ya kwanta dama.

Ɗaya daga cikin masu shirya fina-finai, Husseini Shaibu ne ya sanar da rasuwar tasa a shafinsa na Tiwita ranar Lahadi.

“Na samu sanarwar rasuwar ‘Papa Ajasco’, Mr Femi Ogunrombi daga majiya mai tushe….,” in ji sanarwar.

A halin rayuwarsa, Papa Ajasco ya yi fice a fim ɗin barkwanci mai dogon zango shiryarwar kamfanin Wale Adenuga Production.

Ogunrombi ya maye gurbin jarumi Abiodun Ayoyinka ne a matsayin Papa Ajasco a cikin shirin bayan da Ayoyinka ɗin suka samu matsala da furodusansa.