Gobara ta babbake hedikwatar ‘yan sanda a Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

A yammacin Asabar gobara ta tashi a hedkwatar ‘yan sanda ta Kano da ke unguwar Bompai.

Rahotanni sun nuna gobarar ta tashi ne daga ofishin Provost ta kuma bazu zuwa sashen kuɗi da ɗakin taro da ofishin Kakakin hedikwatar da ofishin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda (Admin) da sauransu.

Mai magana da yawun ‘yan sanda na Jihar Kano, Abdullahi Haruna, ya shaida wa Freedom Radio cewa ba a samu asarar rai ba, kuma wutar ba ta taɓa wasu muhimman takardu ba.

Binciken Manhaja ya gano wutar ta shafi dukkan ofisoshin da ke saman bene na ɗaya na gini in banda ofishin Kwamishinan.

“Mun yi ƙoƙarin kashe gobarar daga ofishin Provost amma sai wutar ta bazu zuwa wasu ofisoshin.

“‘Yan kwana-kwana sun isa wurin ne kusan sa’o’i biyu bayan tashin gobarar,” in ji majiyarmu

By Editor