Bincike ya nuna cewa gida mafi tsada a duniya mallakin Yarima Muhammad Bin Salman ne wanda aka saya a kan Dala miliyan ɗari uku.
Gidan French Chateau an yi gwanjon sa ne a 2015 amma daga bisani jaridar ta gano cewa yarima Muhammad ne ya saye gidan.
An ɓoye wa duniya sanin ko waye ya saye gidan, amma kuma bincike ya bankaɗo yadda aka yi amfani da wasu kamfanoni wanda Yariman ke shugabanta a France da Ludembourg aka sayi gidan.
Tun ba yau ba dai aka sha zargin ’yan gidan sarautar Saudiyya da yin rayuwa irin ta almubazzaranci da dukiyar jama’ar ƙasar ta Saudiyya wanda gidan sarautar Saudiyyar ta sha musantawa.
Jaridar New York Times ta Amurka, ta rawaito cewa Yariman na Saudiyya, Mohammed Bin Salman, shi ne ya sayi wani gida na alfarma a ɓoye a ƙasar Faransa.
Jaridar ta ce, takardun cinikin gidan da aka yi a shekarar 2015, an gano cewa shi ya sayi gidan ta hanyar amfani da wasu ɗumbin kamfanoni da aka yi wa rijista.
Gidan wanda ke daf da fadar shugaban ƙasar Faransa, yana da wurin ajiyar giya na ƙarƙashin ƙasa da sinima da ƙorama da kifaye masu alfarma nau’i-nau’i da wurin shaƙatawa na alfarma da ke ƙarƙashin ƙasa.
Kuɗin gidan dai ya kai dala miliyan 320, wanda mujallar Fortune ta kira shi da gidan da ya fi sauran gidaje tsada a duniya.
Mai magana da yawun ofishin jakadancin Saudiyya a Amurka, ta zargi ma’aikatan jaridar da yin rahoto son rai.
Yarima Muhammad bin Salman na Saudiyya sarkin ƙasar a yanzu, na yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar.
A watannin baya-bayan nan, Yarima Mohammed, ya jagoranci yaƙi da cin hanci da rashawa da cin amanar ƙasa da kuma yadda ake nuna wa wasu gata a ƙasarsa.
A shekarar 2015, an rawaito cewa, yariman ya sayi wani jirgin ruwa na alfarma daga wajen wani hamshaƙin ɗan kasuwa a Rasha a kan kuɗi dala miliyan 590.
Hakazalika, jaridar ta New York Times, ta rawaito cewa shi ne kuma ya sayi wani zane na Salbator Munci, wanda Leonardo da Binci ya yi a kan kuɗi dala miliyan 450.
